24/01/2026
Aslm alaikum 🙏
Barka da safiya gabaki dayan mutanen wannan group mai albarka na makarantar mu, 🏫
Darul hadith wal'uluwm Nasarawa state Akwanga LGA.
Dalililan shigan ka/ki cikin wannan page suna da yawa sosai,
zaku ringa samun recording na karatuttukan mu video da audio wanda mukayi wa
Dalibai a cikin aji, ko masallaci ko guraren wa'azi ko na cikin gida inshallah.
zamu karantar daku tun daga littattafai kanana a fannoni daban-dan kaman su:
Qur'an tajweed, Hadith,Arabic and Arabic grammar,Fiqhu, E.T.C
Fatan mu shine sallaman jahilci daga cikin al-umma da wayar dakai wa mutane izuwaga sunnah
Sannan samarwa daliban ilimi mafita da binciken ilimi a zamanance wato technologia ga fahimtar daku mahimmancin Ilimin zamani dana addini da yanda duniya ke tafiya a yau
Karku manta makarantar mu yanxu muke ginata kuma muna binciko duk wani Ilimi da malamai da makaranta zata cafu sosai a Nigeria harma a duniya baki daya
A karkashin haka dalibai su nutsu su samu kwanciyar hankali da iyayen da suke bibiyar paging mu munada malamai kwararru dazasu karantar daku da tsarukan karantas wa a hannun kowani malami na abunda zai karantar.
Kwanakin baya mun kawo muku jerin sunayen maluman dake tare daku inshallah zamu sake tunatar daku sunayen su da matsayin su a fannin ilimi da kuma kalan gudumawan da zasu baku.
A karshe ina muku fatan alkhairi da nasara a cikin karatun ku.
Media team ✍️
Bross Aminu Ahmed Hamza.