Dr Usman Azare

Dr Usman Azare Welcome to Dr Usman Azare's page! join me in exploring the world of Animal and Public health.

13/10/2023

Rubutun Dr Abdulazizi T Bako

Shafi Mu Lera: Ya abin ya ke a kimiyyance?

Abdulaziz T. Bako, MBBS, MPH, PhD.

An shafe shekaru ana azabtar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba bisa zargin cewa sun sacewa wani yayan maraina ko al'aurar wani namiji ta hanyar siddabaru ko tsafi.

A kan irin wannan zargi maras tushe an kashe mutane masu yawa, an kuma jikkata mutane da dama. Tarihi ya nuna cewa wannan dabi'a an fara ta ne a Najeriya a shekarun 1970s sannan ta yadu a kusan dukkanin sassan kasashen Afirka.

A garuruwan Asia akwai kwatankwacin irin wannan dabi'ar wacce su ke kira 'Koro,' duk da cewa lokaci zuwa lokaci a kan dan samu barkewar cutar kasashen yamma jefi-jefi. Cutar Koro k**ar annoba ce da ta ke sanya wasu sassa na mutane su hakikance cewa tabbas al'aurarsu tana motsewa tana komawa cikin jikinsu, kuma su rika ji cewa idan ba'a yi komai ba al'aurar zata bace bat ta shige cikin jikinsu.

A lokuta da dama mutum daya ne ya ke fara cewa ya ga al'aurarsa tana motsewa, kwatsam kawai sai sauran mutane su ma su ga cewa su ma fa al'aurarsu ta fara motsewa. Irin wannan abu galibi matsala ce ta kwakwalwa (psychological problem) da kan addabi al'umma a lokaci guda wacce a je kira da "mass hysteria."

Sai dai Bambancin "Koro" da shafi mu lera shine cewa su masu Koro galibi ba wani suke zargin cewa ya yi musu asiri ba ballantana su k**a wani wanda bai ji ba bai gani ba da duka. Sannan kuma cutar Koro ba ta ta'allaqa da maza zallaba. Mata ma suna yi. Sai dai da ya ke maganar shafi mu lera muke yi ba zan tsawaita jawabi a kan cutar Koro ba.

Da yawa daga cikin masu zargin cewa an yi musu shafi mu lera su kan ce sun hadu da wani mutum sun gaisa da shi. Sai kuma daga gaisawar s**a ji wani abu ya yi musu yar a jikinsu k**ar shocking. Daga nan kuma sai s**a duba yayan marainansu sai s**a ji babu su.

Daga nan kuma kawai sai su kwarma ihu. Idan mutumin da suke zargi yana kusa su k**a shi a yi ta duka. Idan azaba ta yi azaba sai wanda ake zargin ya yadda cewa ya aikata. Amma zai dawo wa mutum da abinsa bayan wani lokaci. Idan kuwa a ka jirayi lokacin sai a ga ya dawo din. Shikenan sai mutane su gaskata cewa tabbas satar yayan marainan a ka yi.

Kafin na yi bayani a kan yadda wannan abu ya ke faruwa a kimiyyance ya k**ata na yi takaitaccen bayani a kan yadda yayan marainan dan Adam suke samuwa tun yana ciki. Su dai yayan marainan dan Adam farko suna samuwa ne a can saman cikin dan Adam. Daga baya suke sakkowa su yo kasa su zauna a cikin jakar yayan maraina (sc***um) kusa kusa da lokacin da zaa haifi mutum. Shi ya sa wasu yaran idan aka samu matsala a kan haife su da yayan marainan su a ciki ba su sakko kasa ba (undescended te**es).

A yayin da yayn maraina suke sakkowa daga ciki zuwa jakar yayan maraina, akwai abubuwa da yawa da suke biyo su ko don basu kariya ko kuma don wasu dalilai. A cikin wadannan abubuwa akawai wani nama da ake kira da suna Cremaster Muscle.

Kafin mu fadi aikin shi wannan yadin nama na Cremaster Muscle yana da kyau mu gane cewa su yayan maraina ba sa son zafi ya yi yawa ko sanyi ya yi yawa, domin kuwa aikin hada maniyyin dan Adam da a ke yi a cikin yayan maraina (spermatogenesis) ba zai yiwu ba idan zafi ko sanyi ya yi yawa.

Saboda haka sai Allah cikin ikonsa ya halicci shi wannan cremaster muscle din tare da sauran wasu abubuwa k**ar Dartos muscle da su ke tabbatar da cewa zafi ko sanyi bai yi wa yayan maraina yawa ba.

Idan zafi ya yi yawa cremaster muscle ya kan saki jikinsa sai yayan maraina su sakko kasa su sha iska. Idan kuma sanyi ya yi yawa sai cremaster muscle ya motse ya ja yayan maraina sama kusa da cikin dan Adam wanda zai zamewa yayan marainan k**ar heater. Wannan dalilin ne ma yasa a ke baiwa maza shawarar su rage saka matsatstsun dan kamfe (panties) saboda kada zafi ya rika yi wa yayan marainansu yawa.

A halittar shi wannan cremaster muscle akwai abinda a ke kira kuma cremaster reflex, wanda ya ke janyowa shi wannan cremaster muscle din ya motse ya ja yayan maraina sama sama ba wai don saboda sanyi ya yi yawa ba. Abubuwan da suke jawo cremaster reflex sun hada da idan aka shafi wurin jijiyar da ta ke baiwa shi cremaster muscle sak'o, ko kuma abubuwa k**ar matsanancin tsoro da sauransu.

A galibin lokuta shi wannan cremaster reflex ba wani can sama ya ke jan yayan maraina ba, amma a kan samu a wasu tsirarun mutane cewa motsewar da cremaster muscle dinsu ya yi yana da karfi sosai (overactive cremaster muscle), wanda wannan karfin motsewar zai iya sanyawa su ji k**ar shocking a jikinsu, kuma ya ja yayan marainan su koma can sama kusa da mafitsarsu (inguinal region) k**ar zasu koma can cikin ciki (ana kiran hakan retractile te**es).

Idan irin hakan ta faru zata iya yiwuwa a nemi yayan marainan a cikin jakarsu a rasa, amma ba wai sace su a ka yi ba. Su na nan a jikin mutum kawai dai sun yi can sama ne ta yadda ba za a iya jinsu a cikin jakar yayan maraina ba. Kana zuwa wurin likita zai nuna maka inda yayan marainanka s**a makale.

Idan an gane bayanin da na yi a sama to sai mu ce abinda ya ke faruwa shi ne mutum ya gaisa da wani da bai sani ba. Kwatsam kawai sai ya ji cewa fa ya yi kuskure don mutumin nan zai iya zama mai shafi mu lera. Kwatsam sai yanayin tsoro ya k**a shi.

Wannan karfin tsoron da ya ji sai ya saka ya ji yar a jikinsa, shima cremaster muscle ya harba ya motse sai ya ji k**ar an yi masa shocking a yayan marainansa sannan ya ja yayan marainansa sama. Daga nan kuma sai ya taba yayan maraina ya ji ko babu su ko kuma k**ar sun motse daga yadda ya san su da. Shi kenan sai a k**a wani da duka. Azaba ta sa ya yadda cewa ya saci yayan marainan, sannan ya yi alkawarin zai dawo da su. Wannan abin zai kwantarwa da wanda ya ke zargin an sace masa kayan nasa shikenan bayan wani dan kankanin lokaci ya dawo hayyacinsa ya ji komai ya dawo normal (saboda hankalinsa ya kwanta, ba wai don wani ya sace masa wani abu ya dawo masa da shi ba).

Haka abin ya ke ga masu zargin an sace musu al'aura wai ta motse. Shi ma yanayin fargaba ne da tsoro ya ke sanyawa jikin dan Adam ya fara fitar da wasu sinadarai. A gurguje, A jikin dan Adam akwai abinda a ke kira sympathetic nervous system (SNS) da parasympathetic nervous system (PSN). Saboda saukakawa mai karatu ya fahimta, shi SNS shi ke harbawa yayin da mutum ya ke cikin halin firgici da sauransu (fight and flight), shi kuma PNS shi ke harbawa a lokacin da mutum ya ke halin hutu da kwanciyar hankali.

Don haka a yayin da mutum ya ke cikin firgicin tsoron cewa an sace masa al'aura ko kuma al'aurarsa ta motse wannan tsoron ba zai bari ya ji cewa al'aurar tana yadda take ba, saboda a lokacin sympathetic nervous system ne ya ke aiki. Har sai ya samu nutsuwa hankalinsa ya dawo kansa sannan zaa gane cewa babu abinda ya same shi.

A wannan rubutu na saukake (simplifying) abubuwa da yawa saboda na saukakawa masu karatu yadda zasu fahimta. Amma muhallush shahid shine cewa babu wani abu wai shi shafi mu lera. Mu guji azabtar da mutane babu gaira babu sabab saboda wai zargin an sace musu al'aura ko yayan maraina. Duk inda mutum ya yi ihun an sace masa wani abu a yi maza a garzaya da shi asibiti ya ga likita. Babu wanda ya sace masa komai.

LAFIYA JARIN TALAKADARASI NA BAKWAI (07)ZAZZAƁIN JIZON SAURO(MALARIA)ME CECE MALARIA?Wata cuta ce da take k**a mutane da...
19/07/2023

LAFIYA JARIN TALAKA
DARASI NA BAKWAI (07)

ZAZZAƁIN JIZON SAURO(MALARIA)
ME CECE MALARIA?
Wata cuta ce da take k**a mutane da dabbobi sanadiya cizon sauro wacce ƙwayar cuta ta protozoa mai suna plasmodium take haddasawa. Macen sauro dangin Anopheles ce ke da alhakin yaɗa wannan cuta ta hanyar cizon mai ɗauke da cutar ta ɗauko ƙwayoyin cutar bayan sunbi wasu matakai zasu kasance a bakin wannan sauro yanda da taje cizon wani zata cusa masa ƙwayoyin a cikin jinin sa. Amfi samun cutar a ƙasashe masu zafi k**ar na Afirika saboda saurro baya iya rayuwa a gurare masu tsananin sanyi.
IRE-IREN ƘWAYOYIN CUTAR
-Plasmodium falciparum
-Plasmodium vivax
-Plasmodium ovale
-Plasmodium malariea
-Plasmodium knowlesi(zoonotic)
ALAMOMIN CUTAR
Wannan cuta tana fara nuna alamomi ne kwana 8-25 bayan mutum ya kamu da cutar alamomin sun haɗa da:
- Ciwon kai(headache)
- Zazzaɓi mai tafiya ya dawo(recurrent fever)
- Rawar ɗari(shavering)
-Ciwon gaɓoɓi(joint pain)
- Amai (vomiting)
-canjawar kalar idanu yayi ruwan ɗorawa(jaundice)
-Ciwon wuya,
-ciki wani sa'in da kumburi.
IDAN CUTAR TAYI TSANANI ANA IYA GANIN WAƳANNAN ALAMUN

-Gushewar hankali,(unconscioness)
-Zafin jiki da ya wuce degree 39 yayin da aka auna da ma'aunar zafin jiki
-jijjiga sama da sau biyu a awa 24(Convulsion)
-Doguwar suma(Coma)
-Canja kalar fitsari,
-Raguwar zuwa yin fitsari(oliguria)
-Haki ko wahalar numfashi,(Dyspnea)
-Yaushin fata,
-Karancin ruwa ajiki(Dehydaration)
Da sauran su.

YADDA AKE KAMUWA DA ZAZZABIN CIZON SAURO
Ana kamuwa da zazzabin ne yayin da
-Sauro ya ciji mutun,
-Tahanyar karin jini,
-Daga uwa zuwa danta alokacin da yake ciki(congenital malaria).

WADANDA SUKAFI SAURIN KAMUWA.
-Yara kasa da shekaru biyar da Manya Yan sama da shekaru 65,
Wadanda garkuwar jikinsu tai kasa k**ar masu ciwon hiv,suga,masu ciki da masu ciwon sikla.
ILLAR ZAZZAƁIN CIZON SAURO
Akowace shekara aƙalla sama da mutane million 300 ke kamuwa da zazzaɓin cizon sauro,aduk cututtukan da ake fama da su a duniya zazzaɓin cizon sauro shine nafarko wajen kawo mutuwar yara kananu kasa da shekarawa biyar. Yara sama da 80,000 ke mutuwa a Africa saboda cizon sauro.Hakazalika Sama da 40,000 cikin wanda ke warkewa na fama da matsalolin kwakwalwa. A nigeria kaso 30 cikin 100 da ake kwantarwa a asibiti adalilin zazzabin cizon sauro ne,sannan kuma kaso 60 cikin dari da ke zuwa asibiti Shima duk dalilin wannan zazzabine.

GAGGAWAR ZUWA ASIBITI
Idan yaronka ƙarami dan ƙasada shekar biyar kaga yana zazzaɓ ko wasu daga cikin alamomin can ko kuma mace mai ciki to kayi gaggawar kaisu asibiti saboda yanda wannan cuta take saurin hallakasu. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.
Usman Muhammad Hakimi
29 September, 2022.

LAFIYA JARIN TALAKADARASI A SHIDA(06)TARIN FUKA/ TARIN TB (TUBERCULOSIS)MENENE TARIN FUKAWata cuta da ƙwayar halitta ta ...
19/07/2023

LAFIYA JARIN TALAKA

DARASI A SHIDA(06)

TARIN FUKA/ TARIN TB (TUBERCULOSIS)

MENENE TARIN FUKA
Wata cuta da ƙwayar halitta ta bacteriya mai suna Mycobacterium tuberculosis(Asalin ta mutane) ko Mycobacterium bovis(wacce ake samu daga shanu)take haddasawa, dama wasu sauran nau'ukanta. Cutace mai yaɗuwa a tsakanin mutane da dabbobi, cutace da take ci a hankali a hankali in ta kai maƙura tana kashe marar lafiyan da ke ɗauke da ita. Huhu take k**awa amma tana iya k**a sauran kayan ciki k**ar su hanta, saifa da sauransu.

HANYOYIN ƳAƊUWAR WANNAN CUTA
1-cutar tana ƴaɗuwa ta hanyar iska idan mai ɗauke da cutar yayi
Tari
Atishawa
Fesar da majina
2- Shan nonon Saniya mai ɗauke da cutar
3- Cin huhun saniya ko wata hanta mai ɗauke da cutar
4- Mu'amala ta kusa da kusa tsakanin dabba mai ɗauke da cutar(closed contact)
5- Cutar HIV/AIDS- masu ɗauke da wannan cuta suna saurin kamuwa da cutar TB

ALAMOMIN WANNAN CUTA
-Tari na inna naha(chronic cough)
-Kaki mai jini(blood tinge sputum)
-Zazzaɓi(fever)
-Zufa/gumi cikin dare(night sweat)
-Ramewa/ƙeƙashewa(weight loss/Emaciation)
-Ciwon ƙirji

ABUWAN DA KE TAIMAKAWA A KAMU DA CUTAR(RISK FACTORS)
-Cunkoso(overcrowding)
-Cutar yunwa(malnutrition)
-cutar Sida(HIV)
-Shan ƙwaya(drug abuse)
-Shan taba/sigari
- Ma'aikatan lafiya masu kula da masu cutar mussaman in basu amfani da matakan kariya
-Ciwon huhu mai tsanani(chronic lung disease)
- Shan giya(alcaholism)
-Ciwon suga(diabetes mellitus)
Da sauransu

MAGANIN WANNAN CUTA
Wannan cutar tana da wahalar magani saboda yanayin halittar bacteriya ɗin yana hana antibayotic(antibiotic) da yawa shiga cikinta ya kasheta. Suma wanda suke kashe ta ana ɗaukan tsawon lokaci wata da wattani ana maganin kafin ta warke.

HANYOYIN RAGE YAƊUWARTA(PREVENTIVE MEASURES)
1 Rigakafi(vaccine)
-2 Wayar da kan mutane (public enlightnent):
- mussamman fulanin mu masu kafa kai a bakin nonon saniya su sha
- kwatar da ake yanka shanu ba tare da kulawar likita ba(veterinarian supervision)
da sauran su.
Usman Muhammad Hakimi
28 September, 2022.

LAFIYA JARIN TALAKADARASI NA HUƊU(04)MACIJI, SARAN MACIJI, TAIMAKON GAGGAWA GA WANDA MACIJI YA SARASHEMACIJIKamar yadda ...
19/07/2023

LAFIYA JARIN TALAKA

DARASI NA HUƊU(04)

MACIJI, SARAN MACIJI, TAIMAKON GAGGAWA GA WANDA MACIJI YA SARASHE

MACIJI
Kamar yadda duk muka sani maciji wata halittace mai jan ciki marar ƙafafu dake cikin dangin hallittun da ake ƙira carnivorous reptiles( haliitu masu saɓa da ke cin nama). Anfi samun macijai a ƙasashe masu zafi(tropical regions) amma ana samun su a dukka ƙasashen duniya banda yan kaɗan k**ar: Antarctica, Ireland, Iceland, Greenland, New Zealand da wasu ƙasashen kan tudu masu tsananin sanyi.

DAFIN MACIJI
Kashi 70 cikin ɗari na macijan duniya basu da dafi, Kazalika sauran kashi 30 ɗin suma kusan kashi 50 cikin 100 na saran da sukeyi basa zuba guba (dry bite ne).

DAFI: wata guba ce da hallitu da yawa suke dashi kuma suke amfani dashi wajen kare kansu daga masu cutar dasu, ko kuma domin su, su cutar da wata hallitar. Na Maciji yana ƙunshe da sinadarai masu yawa wanda s**a haɗa da(proteins, peptides, polypeptides,carbohydrates, lipids, nucleosides, biogenic amines, free fatty acids ,magnesium, calcium, da zinc).

MAJIZAI MASU GUBA(DAFI) A NAJERIYA
Ana kasa majizai masu dafi a Najeriya zuwa kashi huɗu ko wanne kashi yana ɗauke da majizai masu tarin yawa amma dai zamu fi maida hankali akan macizai uku mafiya hatsari daga cikin wayannan kashe kashen sune k**ar haka:
1- Echis occelatus (carpet viper)- Da hausa:Kububuwa, Gobe da nisa, gajera, Tafakasa.
2- Bitis arietans ( puff udder) -Da hausa: Kasa
3- Naja nigricolosis (black spitting cobra)- Da hausa Baƙi.

Wayannan majizai guda uku kusan kashi 90 na mace-mace sak**akon saran maciji to sune sanadi. Zan saka hotunan su a ƙasan wanna rubutu domin ganesu.

HATSARIN SU:
1- Na farko ɗin nan wato kububuwa gajeriya ce mai ruwan ƙasa-ƙasa wani lokacin toka-toka tana ɓuya acikin busassun ganyayyaki, ƙasan dutsi, gefe-gefen daji mai surƙuƙi, tana da sauri k**ar iska da saurin kawo sara. Tana ɗauke da dafi mai hatsari da yake tsinka jini, kaga jini yana zuba ta baki, ta hanci, ta dubura, wani lokacin har ta ido. Itane lamba ta ɗaya a wajen kashe mutane a cikin majizai a Najeriya.
2- Ta biyu wato Kasa; tana da kaloli da yawa da s**a haɗa da ruwan ƙwai, ruwan ƙasa-ƙasa, ko kalar lemo, tan da facin baƙi-baƙi a bayanta. Tana iya kaiwa tsayin mita ɗaya da digo takwas, da daddare take fitowa kiwo da rana ta ɓuya ta yi bacci, tana da saurin kaiwa sara a duk wanda ya nufi kanta. Tana sajewa da busassun ganyayyaki idan ba'a lura ba. Dafin ta yana shiga can ciki jiki ya tsinka jini kuma ya ɓata nama. Saran ta yana haifar da matsaloli da yawa da s**a haɗa da bugawar zuciya, toshewar numfashi, rikicewar tunani da saɓa a fata. Yawan dafin da take zubawa mutum ɗaya zai iya kashe mutum huɗu in aka sa musu shi.
3- Ta uku wato baƙi asali ba shine Gamsheƙa ba amma yan gida ɗaya ne shi yasa wasu basa banbance su, su ke ƙiran su da suna ɗaya. Shi baƙiƙƙirin ne duk da a wasu ƙasashen ana samun sa ja-ja ja-ja. Amma dai babbar hanyar ganeshi shine yana da wani jan layi a ƙasan wuyansa. matsakaici ne zuwa jibgegge. Anasamun sa a gurin da akwai tana da yawa ko gafiyoyi da beraye da ƙadangaru. Yana hawa bishiya kuma yana shiga ruwa. Dafin sa yana ruɓar da nama kuma yana feshi a cikin idon mutum na dafin sa.

SAURAN MACIZAI MASU DAFI A NAJERIYA
Dispholidus typus, Boomslang (Hausa- sagon doka)
Elapsoidea semiannulata: Angolan Garter Snake (Hausa Kwadaddafi)
Naja haje: Egyptian Cobra (Hausa: Gamsheka)
Naja katiensis, Mali Cobra, Katian Spitting Cobra (Hausa: Jan nashuri)
Naja melanoleuca ( Black and White Cobra. Hausa – Bakaya,
Pseudohaje nigra, Hoodless Cobra (Hausa Tsadaraki)
da sauran su

TAIMAKON GAGGAWA GA WANDA MACIJI YA SARA
A al'adance musammam a kauyukan mu gunda saran maciji yafi yawa suna aikata wayannan al'adu da sunan taimakon gaggawa amma bincike na kimiya ya tabbatar da cewa basu da al'afanu sai ma illla da suke iya haifarwa k**ar su ɗaure gurin da macijin ya sara da tsumma da ƙarfi, ƙoƙarin zuƙe jini/dafi daga gunda akayi saran, yiwa marar lafiyan shokin da lantarki, wanke gurin da ruwa, Dukka wannan ba abin da sukeyi sai ƙara jinkiri wajen cetoshi a asibiti.

ABIN DA AKE SO AYI
1 kwantarwa da marar lafiyan hankali- saboda damuwa da tashin hankali ba abin da sukeyi sai ƙara sawa dafin yayi saurin yaɗuwa
2 Ayi ƙoƙarin wajen ganin yanda za'ayi ya dena motsa kafar ko hannun da macijin ya sara kuma a nannaɗeshi da bandeji
3 Ayi gaggawar kaishi Asibiti amma cikin nutsuwa ta yanda ba za a jijjagashi ba.
Dukka wanna domin a rage damar yaɗuwar dafin ne a cikin jikin sa. kuma wannan ya shafi mutum ko dabba da macijin ya sara.
WANDA MACIJI YAYI WA TSURTUWA A IDO
Ayi gaggawar wanke masa idanun kafin dafin ya fasa namam idon ya fara shiga ciki, wankewar ana yinta da ruwa mai gudana da ƙarfi k**ar na fanfo in dai anyi haka cikin sauri to ba abin da dafin zai masa amma duk da haka yaje yaga likita. Idan abin ya faru a cikin jeji gunda ba ruwa to a samu wanda yake jin fitsari ya seta idon ya tsula masa fitsari da ƙarfi, fitsarin zai wanko dafin, laruri ne yana halasta haram.

MAGANIN SARAN MACIJI
Magani ɗaya da hukumar lafiya ta duniya ta amince dashi a matsayin maganin dafin maciji shine Antivenom sai dai yana da ƙaranci da matuƙar tsada musamman a ƙasashe masu tasowa. Allah ya bamu yanda zamuyi ya kuma kare mu daga saran na maciji.

Usman Muhammad Hakimi
26 September, 2022.

LAFIYA JARIN TALAKADARASI NA UKU (03)MURAR TSUNTSAYE ( AVIAN INFLUENZA, AVIAN FLU)Wannan cuta tana kashe sama da kashi 6...
19/07/2023

LAFIYA JARIN TALAKA

DARASI NA UKU (03)

MURAR TSUNTSAYE ( AVIAN INFLUENZA, AVIAN FLU)

Wannan cuta tana kashe sama da kashi 60 cikin ɗari na mutanen da tak**a

MECECE MURAR TSUNTSAYE?
Wannan wata cutace wadda ƙwayar halitta ta virus mai suna "Influenza A virus" dake k**a illahirin tsuntsaye k**ar: kaji, tattabaru, agwagi, zabi, dawisai, jiminoni, talotalo da sauran nau'ukan tsuntsaye na gida dana daji.

Ƙwayar cutar ana rabata a jimlace zuwa kashi biyu
1 High pathogenic Avian influenza(HPAI)
2 Low pathogenic Avian influenza (LPAI)
kashi na biyu na wannan cuta ana samun sa a dukka sasan duniya kuma tana da sauƙin sha'ani bata da illah sosai ga su tsuntsayen dama mutane. Yawancin tsuntsaye mu da suke kiwo na yawo a bayan gidajen mu (free range birds ko backyard poultry)suna da wanan cuta musammam wanda suke masu yawo daga wata nahiyar ta duniya zuwa wata (migratory birds) k**ar shamuwa, mikiya da sauran su.

Kashi na ɗaya na wannan ƙwayar cuta shine mafi hatsari ga su tsuntsayen dama mutanen da s**a kamu. Tana bulla daga lokaci zuwa lokaci ko kuma daga guri zuwa guri abin da ake kira(outbreak)

TA YA TAKE BULLOWA?
-Mafi akasari wild life birds(tsuntsayen jeji) ko migratory birds( tsuntsaye masu yawo daga nahiya zuwa nahiya) su suke ɗauko cutar su yaɓawa namu tsutsayen na gida. Idan ƙwaya ɗaya daga namu tsuntsayen ya kamu to duk yawan tsuntsyen dake tare dashi zasu kamu hakanan ma har zuwa tazarar kilomita 10 duka iska zata iya ɗaukar ƙwayar haliitar ta kai,misali
-Kaza zata iya kamuwa da cutar a Maiduguri a ɗauke ta akaita Abuja da niyar sayarwa ta shafawa duk tsuntsayen da s**a mu'alamceta a Abujan ko hanyar ta.
-Ƙwasar kayayyakin amfanin gona da cutar ta ɓulla zuwa wani guri ka iya yaɗa wannan cuta
-Kajin mu ko sauran tsuntsayen mu irin tattabaru da muke bari suna yawo kara zube suna iya ɗauko wannan cuta a yawon su suyi ta yaɗa ta ba ƙaƙƙautawa.
Sauran dabbobin da suke kamuwa da wanan cuta sun haɗa da:
Zomaye, Beraye, Beran masar, Aladu, Birrai da sauran su

ALAMOMIN WANNAN CUTA
-Kumburin kai, muƙamuƙi, kyarkyara(comb and wattle) da ƙafafu.
-Alamun mura irin su tari,atishawa, toshewar numfashi.
- Yawan mutuwa ta innanaha( gonar kaji guda tana iya ƙarewa a cikin kwana uku)
- Rashin daidatuwa ta gaɓoɓin jiki( incoordination)
- Karyewar wuya( torticollis)
- shanyewar jiki( paralysis)

HANYOYIN KARIYA DAGA WANNAN CUTA (PREVENTIVE MEASURES)
1-Biosecurity- wasu matakai ne da ake ɗauka domin kare gona daga shigar cuta sun haɗa da
-Kewaye gonar da katanga da rufi da net ta yanda ƙwari, ƙadangaru ko tsutsayen jeji baza su iya shiga ba
-Sanya kaya na musamman domin shiga gonar- kayan ana aje su a gonar ne
-sanya maganin kashe ƙwayar cuta a ƙofar shiga gonar ta yadda duk mai shiga zai bi ta ciki da takalmin sa
-Taƙaita shigar baƙi cikin gonar
- tsaftace gonar da kuma feshi na kashe ƙwayoyin cuta. Da sauran su

2- Rigakafi a ƙasashen da sukeyi- Nigeria bata ciki (rigakafi yana jawo illoli da yawa k**ar yanda aka gani a ƙasashen da sukeyi irin ƙasar Masar)

MATAKAN DA YA KAMATA A ƊAUKA BAYAN CUTAR TA BAYYANA(CONTROL)
1-Gaggauta sanar da hukumomi dangane da ɓarkewar cutar
2- Jamian kiwon lafiya na sashin dabbobi zasu zo su tabbatar
3- Stamping out( kashe illahirin kajin da suke wannan gona da kuma aƙalla kaji da sauran tsuntsayen da suke kilo mita 10 daga wannan gona ta ko wanne ɓangare kudu da yamma gabas da arewa). Wannan shine abin da akeyi a ƙasashen da s**a ci gaba.
4- Gwamnati zata biya diyyar dukka kajin da aka kashe
5-Modified stamping out( shine abin da ƙasar mu ta Nigeria take yi a yanzu, tana kashe kajin iya gonar da aka samu bullar wannan cuta ne saboda ragewa kanta kuɗin diyya)
ILLAR WANNAN CUTA GA MUTANE(ZOONOTIC RISK)
k**ar yanda wannan cuta take kashe tsuntsayen da tak**a hakanan ma take kashe da yawa daga wanda ta k**a a cikin mutane, ana kamuwa da ita ne ta waɗannan hanyoyi:
- Mu'amala ta kai tsaye da rayyaye ko mattacen tsuntsu mai ɗauke da wannan cuta(Direct contact)
-fige gashin tsuntsun da ya mutu ta sanadiyar cutar
- Cin naman tsuntsu mai ɗauke da cutar
-Mu'amala da mutumin da ya riga ya kamu da cutar ba tare da matakan kariya ba
- Hukumar lafiya ta duniya bata amince da wani magani da za'a bayar da niyar maganin wannan cuta ba.
Zamu taƙaita haka badan bayanan sun ƙare ba.

Usman Muhammad Hakimi
25 September, 2022.

Address

Gombe Road
Azare
751101

Telephone

+2349063162393

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr Usman Azare posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category