06/08/2026
Ni Atiku Muhammad daga Jihar Kebbi. Ina da lalurar tafiya, kuma malami ne a makarantar firamare. Na kammala karatun NCE, sannan ina ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar masu buƙata ta musamman ta JONAPID. Haka kuma ni ne Babban Sakatare (General Secretary) na ƙungiyar Disables APC Awareness for People with Disability.
Ina kira ga duk masu buƙata ta musamman da kada su ji tsoro ko kunyar fitowa cikin al'umma. Mu ma 'yan ƙasa ne masu cikakken ikon bayar da gudunmawa wajen ci gaban al'umma. Nakasa ba ta hana mutum zama mai amfani ga kansa da ƙasarsa.
Na taɓa haɗuwa da wata mata mai suna Amina Muhammad, wadda ta samu lalurar rashin iya tafiya daga baya a rayuwarta. Saboda damuwa da kunyar halin da take ciki a ganta tana rarrafe, ta daina fita cikin jama'a, har ta kai ga tana rayuwa cikin keɓantuwa.
Na ziyarce ta, na ba ta shawarwari, na ƙarfafa mata gwiwa, sannan na haɗa ta da wasu mata masu irin wannan lalura. Ta koyi sana'o'in lalle da kitso, sannan na taimaka mata da jarin fara ƙaramar kasuwanci.
A yau, Amina ta daina jin kunya, tana gudanar da rayuwarta cikin walwala kamar kowa, kuma tana dogaro da kanta. Wannan ya tabbatar da cewa nakasa ba kasawa ba ce, sai dai ƙalubale da za a iya shawo kansa da ƙoƙari, ilimi da goyon baya.
Ina kira ga masu buƙata ta musamman da su fito su shiga harkokin siyasa, su zama jakadun al'ummarsu, su nemi ilimin zamani da na addini, tare da koyon sana'o'i domin su dogara da kansu.
Lokaci ya yi da za mu nuna wa duniya cewa muna da baiwa, ƙwarewa da damar ba da gudunmawa kamar kowa.