Lambun Ma'aurata

Lambun Ma'aurata Shafi ne domin tattaunawa kan matssalolin zamantakewar aure da nufin gano bakin zaren wajen warwarewa

Allah ya maimaita mana.baɗin-baɗaɗa
28/05/2026

Allah ya maimaita mana.baɗin-baɗaɗa

Kowane miji da irin kyautar da.yake ɓayarwa a matsayin kayan faɗar kishiya. Wasu na yawan biyawa matansu kujerar Hajji d...
22/05/2026

Kowane miji da irin kyautar da.yake ɓayarwa a matsayin kayan faɗar kishiya. Wasu na yawan biyawa matansu kujerar Hajji domin dannar ƙirji. Shin idan ƙaɗɗara ta afko aka biya miki kujerar Makka a matsayi kayan faɗar kishiya za ki je kuwa, ko kuma fushin Majiɓare za ki yi?

Akwai wadda aka bata zaɓi tsakanin kujerar Makƙa da kuma Mota Tuwaris, sai ta gwammace bazawa amarya kapasiti da mota gwanjon Turawa akan zuwa sauke farali a yanzu dai babu motar saboda masifar tsadar mai, ga kuma kujerar maka ta kusan kaiwa miliyan 9. Biyu baɓu kenan tagwayen rasassu.

Wasu kuma mazajen suna sayawa matansu gida ko su ba su kyautar ploti duk don dannar ƙirjin zuwan kishiya.

Wata ma ɗan sahu aka saya mata aka ƙwaɗaita mata batun samun balance duk sati, nan take ita kuwa ta dinga murna tana washe baki kamar wadda ta ci aya.

Kowa da irin ƙaddararsa. Idan mai gidanki yana son ƙarin aure kada ki kuskura ki ɗaga hamkalinki. Ƙarshe idan kin hana shi sai ya fara ha'intarki, duk da mun san akwai masu cewa da auren sunnah gwanda haramtacciyar zina. Eh mana! Wannan shi ne cikakkiyar fassarar batun nan na: "da kishiyar gida gwanda ta waje" da wasu shaiɗanun mata suke yawan faɗa gabansu gaɗi ba ko jin kunyar ma'anar hakan.

Allah yai mana mai nice duniya da lahira! ❤❤❤

Me yasa ake yi wa duk wadda mijinta ya ke nuna mata tsagwaron ƙauna hassada da ƙyashi?Idan kuma ita matar ce take nuna ƙ...
20/05/2026

Me yasa ake yi wa duk wadda mijinta ya ke nuna mata tsagwaron ƙauna hassada da ƙyashi?

Idan kuma ita matar ce take nuna ƙaunar mijinta sai a diinga kiranta da sunaye irin su 'miji-daɗi'?

Wasu fa ko jerowa s**a ga miji da mata sun yi, za su unguwa, gwanin sha'awa sai abar ta motsa, ku ga sun fara wasu muzuran iska, suna ta wani faman harare-harare kamar an ci musu wani abu ba a biya ba.

20/05/2026
Zaɓi-ka-tiƙa, sunan wata jarrabawar ƴan makarantar boko:
20/05/2026

Zaɓi-ka-tiƙa, sunan wata jarrabawar ƴan makarantar boko:

"Kunya tana daga cikin imani!"
20/05/2026

"Kunya tana daga cikin imani!"

SANARWA:Assalamu alaikum ƴan uwa.Muna son yau ɗaya dai a nuna mana kara aje ayi wa shafin nan namu mai albarka reviews. ...
20/05/2026

SANARWA:

Assalamu alaikum ƴan uwa.

Muna son yau ɗaya dai a nuna mana kara aje ayi wa shafin nan namu mai albarka reviews. Tunda aka buɗe shi a 2021, ba mu taɓa samun review ko da guda ɗaya tak ba.

Reviews ɗin ƙuma suna da matuƙar amfani wajen nuna ingancin shafi da cigaba da yaɗa shi ga sauran jama'a don su ma su amfana.

Ga hoto nan an kewaye wajen da jar tawada.

Wannan tauraron za a latsa zai nuna duk matakan da ake bi don cikewa, a can ƙarshe ƙuma ana son ayi share.

Kawai ƴan kalmomin yabo da gamsuwa da jin daɗi game da shafin ake son a rubuta, ko da wane yare kuma aka yi babu damuwa.

Mun gode ƙwarai. Da fatan ba za a watsa mana ƙasa a ido ba.

Muna ƙara godiya da cigaba da kasancewa da mu a wannan shafi mai albarka na

Lambun Ma'aurata

Layya Sunnace Ya ku Ma'aurataDuba da yanayin halin matsin rayuwar da ƴan siyasa s**a jefa al'ummar Najeriya da gangan, y...
20/05/2026

Layya Sunnace Ya ku Ma'aurata

Duba da yanayin halin matsin rayuwar da ƴan siyasa s**a jefa al'ummar Najeriya da gangan, ya ke ƴar uwa, bai kamata ki tashi hankalin mai gidanki ba idan alamu s**a nuna cewa bana ba za a samu damar yin layya ba.

Layyar nan fa daman sunnah ce kuma ko ƙarfin shafa'i da wuturi bata kai ba a sunnance.

Allah ya horewa kowa, ya kawo mana ƙarshen duk wata damuwa.

Jagorar Iyaye don Fahimtar Alamomin Halayya da na Jiki na Matashiyar da aka Fara NemaWannan bayanin an tsara shi ne daga...
09/05/2026

Jagorar Iyaye don Fahimtar Alamomin Halayya da na Jiki na Matashiyar da aka Fara Nema

Wannan bayanin an tsara shi ne daga mahangar kwararru a fannin Masana Halayyar Dan Adam (Psychologist) da kuma Masanan Lafiyar Jima'i (S*x Therapist) domin taimaka wa iyaye fahimtar sauye-sauyen da ke faruwa da 'ya'yansu matasa.

1. Alamomi masu Alaƙa da Halayya da Ruhi A kimiyance, matashiya kan fuskanci wani irin nauyi a zuciya lokacin da take ƙoƙarin boye wani babban sirri kamar jima'i. Ga abubuwan da ya kamata a lura da su:

Yawan Kebewa ita Kaɗai da kuma Boye-boye ko Nuƙu-nuƙu da Ƙumbiya-ƙumbiya: Idan yarinya ta fara garkame kofa a kowane lokaci, ko kuma tana firgita idan aka shigo dakinta ba zato ba tsammani ta yi wnai wuri-wuri da.ƙifo-ƙifi da idanu. Haka kuma, idan aka lura tana nuna tsananin kula da kaffa-kaffa ga wayarta (kamar sanya lambobin tsaro na sirri da take canjawa akai-akai).

Sauyawar Yanayi: Bincike ya nuna cewa matasan da ke jima'i a boye s**an kasance cikin matsamanciyar damuwa ko fushi na ba gaira babu dalili saboda tsoron kada asirinsu ya tonu ko kuma fargabar daukar cikin shege.

Canjin Ƙawayei: Tana iya fara nisantar kawayenta na kwarai, ta fara mu'amala da wadanda s**a girme ta ko wadanda suke da halaye na 'yanci da ya wuce kima.

Karya da Yaudara: Idan yarinya ta fara yawan bayar da hujjoji marasa tushe na inda ta tafi ko kuma tana yawan latti wajen dawowa gida daga makaranta, to tabbas akwai lauje cikin naɗi, ba mamaki tuni har an fara bata lambar ɗakin hotel tana kai kanta wasu ƙattin banza suna sanƙama son ransu.

2. Alamomin Jiki: A bisa ga mad9garar masana lafiyar jima'i, muna ba da shawarar lura da wadannan batutuwa na zahiri:

Sauyi a Tsarin Al'ada (Menstrual Changes): Damuwa da fargaba na iya sa al'adar matashiya ta rinka rikice wa. Haka kuma, idan ta fara amfani da kwayoyin hana daukar ciki a asirce, hakan na iya canza tsarin jikinta.

Alamomi a Fata : Lura da shatun mazauni ko "hickeys" (shatun tsotsa) a wuya, kirji, ko cinyoyi. Yawancin matasa s**an rinka sanya tufafi masu rufe jiki sosai (ko da kuwa lokacin zafi ne) domin boye wadannan alamomin.

Rashin Jin Dadi a Gabobi: Idan tana yawan korafin ciwon mara, radadi lokacin yin fitsari, ko kuma kaikayin gaba. Wadannan na iya zama alamomin rauni ko kuma kamuwa da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i (STIs).

Samun Abubuwan Boye: Kamar samun ledar kwararo roba (condoms), kwayoyin hana daukar ciki na gaggawa (emergency pills), ko magungunan wanke sanyi a cikin jakarta ko dakin baccinta, ko magungunan da matan aure suke kira na gyara don kumbura sha'awa da.ƙarin ni'ima a ɗakinta ko jakarta.

Sauyi a Fatar Jiki: Aɓinda mutane da yawa basu sani ba shi ne shi jima'i kamar chemistry ne. Harka ce mai cike da tasirim wasu sinadarai daban-daban masu kowa sauyi mabayyanina jikin duk wadda ake saduwa da ita. Ruwan namiji kan bayar da wasu manyan sinadarai da ke aiki kai tsaye a jikin wadda s**a sadu da ita kai tsaye, ko kuma su tunzura jikinta ya fara zubar da ruwan wasu sunadarai masu sauya yanayin sheƙin fata da alamun ni'ima da jin daɗi a jikinsu ba tare da ma sun sani ba. Amma sai dai kuma duk masana da manya fa suna gani sun san komai sai dai su ja baki su yi shuru ko suyi addu'ar Allah ya shirya a zuci.

3. Matakan Da Ya Kamata Iyaye Su Dauka Maimakon yin fada ko hukunci mai tsanani, kwararru suna ba da shawarar:

Tattaunawa ta Hikima: Kada ku tuhume ta kamar mai laifi. Ku nuna mata cewa kun lura da canjin yanayinta kuma kuna son taimaka mata ne.

Ilimantarwa: Ku ba ta sahihin ilimin jima'i (S*x Education) da illolinsa na addini, zamantakewa, da kuma lafiya (kamar ciki da cututtuka).

Gina Alaƙar ta Aminci: Matashiya za ta daina boye sirrikanta ne kawai idan tana jin cewa iyayenta abokantaka ta janta a jiki za su nuna mata, ba wai tsana ko cin mutunci ba.

Lura: Wadannan alamomin ba lallai ne su zama tabbataccen shaida a kowane lokaci ba, domin wasu cututtuka ko matsalolin tashen balaga kan iya janyo wasu daga cikinsu. Neman shawarar likita ko masanin halayya shi ne abu mafi a'ala.

Mutum ake kiwo ba dabba ba.

Allah ya shiga tsakanin nagari da miyagu!

Yayinda lalata tafi aure sauki, to ku jira abinda zai faru......
09/05/2026

Yayinda lalata tafi aure sauki, to ku jira abinda zai faru......

Shin wai me ƴan matan wannan zamanin suke nufi idan s**a ɗora hoton wata kyaƙkyawar ƙawarsuɓa status kuma s**a bi ahi da...
08/05/2026

Shin wai me ƴan matan wannan zamanin suke nufi idan s**a ɗora hoton wata kyaƙkyawar ƙawarsuɓa status kuma s**a bi ahi da wasu zafafan kalaman so da ƙauna kamar na miji da.matarsa?

Kada fa ace lalacewa tamu har ta kai an daina yin daudancin mata a ɓoye an fara fito da komai gaban kowa ido na ganin ido.

Ba wani ɗan auren da zai ƙi aure, sai dai idan akwai lauje cikin naɗi a tarihin samuwarsu.

Address

Nasarawa GRA
Gra

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lambun Ma'aurata posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Lambun Ma'aurata:

Share