05/08/2026
ILIMIN LAFIYA 012
Muhimmancin Gujewa Shan Sigari da Sauran Abubuwan Da Ke Cutar da Lafiya.
AL-AMANA HEALTH AWARENESS.
Shan sigari da amfani da wasu abubuwa masu cutar da lafiya na iya jawo matsaloli ga huhu, zuciya da sauran sassan jiki. Guje musu yana taimakawa wajen kare lafiya da inganta rayuwa.
Fa'idodin Gujewa Sigari.
🫁 Yana taimakawa kare huhu.
❤️ Yana rage haɗarin cututtukan zuciya.
🌬️ Yana sauƙaƙa numfashi.
👨👩👧👦 Yana kare lafiyar iyali daga hayaƙin sigari.
💰 Yana rage kuɗin da ake kashewa kan abin da ke cutar da lafiya.
A Shawarce:
✅ Idan kana shan sigari, ka nemi taimakon ƙwararren ma'aikacin lafiya domin dainawa ta hanyar amfani da shawar wari.
✅ Ka guji zama a wuraren da ake shan sigari domin kare kanka daga hayaƙin sigari.
Mu Tuna
Guje wa sigari da sauran abubuwa masu cutar da lafiya na daga cikin matakan kare kai da iyali.
AL-AMANA ISLAMIC AND MODERN TRADITIONAL MEDICINE
Lafiyarku, Amanarmu.
✍️ Dr. Ibrahim Al-Amana
📞 🇳🇬 08100227103
📞 🇳🇬 09040845654
📞 🇳🇪 +227 77746842
DrIbrahimAlAmana