09/03/2024
Saƙo Ga Sabbin Angwaye Da Masu Niyar Aure.:
Ganin Jini A Daren Farko Bashi Ne Budurci Ba:
A zamanin da can, anyi lokacin da ake shinfida farin kyale akan shifidar sabbin ma'aurata domin a tabbatar da budurcin amaryar.
Idan jini ya zuba a daren farkon saduwarta da mijinta to wannan itace budurwa abar alfahari ga iyayenta dama zuri'ansu gaba daya. Idan kuwa ba a ga jini ya malale wannan farin kyalen ba to wannan amaryar ba budurwa bace aka auro, ma'ana tana zina ko ta taba yin zina. Wanda hakan na iya rusa wannan auren.
Wannnan maguzanci tonon silili yayi tasiri sosai cikin wasu kabilun African ciki harda kabilun Hausa da Fulani. Wanda tasirinsa ya jima cikin al'uma sosai kamin kungiyoyin addini su yaki irin wannan bakar al'adar.
Wasu mazan suna dauka cewa muddin basu ga jini ya zuba a darensu na farko da sabuwar amaryarsu ba to a tunaninsu wannan amaryar ta taba yin zina ko kuma tanayin zina.
Wasu mazan kuwa suna daukar cewa muddin basu sha wahala ba wajen shigar da azzakarinsu farjin amaryarsu a daren farko wannan ma alamune na amaryar tana zina. So suke suga a ranar farko babu kofa a farjin amaryarsu sai sun shiga da kyar.
Wannan camfin ko tunani da har yanzu yake da tasiri ga wasu mazan yasa yanzu haka 'yan mata masu niyar aure wandan kuma s**a taba zina ko suke zina suke da dabaru da damar gaske da suke amfani dasu wajen tsuke gabansu ya dawo tamkar na yar shekaru 7 da haihuwa.
A yanzu haka akwai hanyoyi na zamani dana gargajiya masu yawan gaske da 'yan mata suke bi kuma suke amfani dasu domin su tsuke gabansu har sai jini yayi zuba a daren farko aurensu. Inda ango sai yayi ta murna da farin cikin ya samu matarsa a budurwa nan ko baisan dawan gari ba.
Sai dai kuma yana da kyau maza su fahimci cewa ita fa budurwa da akwai hanyoyi masu yawan gaske da zata iya fita daga budurci kuma batasan wani danamiji da sunan jima'i ba.