10/06/2021
TAFASA
MA'ANAR TA
Da Hausa ana kiran ta da sunaye kala-kal k**ar:
Tafasa,
Albarka, da
'Yar-malam,
Da Yarabanci kuwa suna ce mata:
(JELEMUBENU).
Da Inyya-muranci kuwa (igbo) suna ce mata:
(AKPUKA UMUAKA).
Da Turanci ana kiran ta:
(FOETID CASSIA).
Da Kimiyya kuma ana kiran ta:
(CASSIA TORA).
Haka kuma Tafasa 'yar dan gi ce, tana da 'yan-uwa da yawa a dangin su, wadanda s**a fito a rukuni ko Dangi daya. Ana kiran sunan Dangin su (FAMILY NAME) da:-
(LEGUMINOUSAE CEASALPINACEAE).
Ire-iren Dangin su sun hada da:
Rai-dore, Runhu, Magarya, dorawar-bature, Kargo, Gwaska, Maje, da sauran su.
KAMANNIN TAFASA (Description):
Tafasa ciyawa ce: wacce tsawonta yakan kai mita daya da digo bakwai (1. 7m), kuma tana da rowan-dorawar huda, sannan gayan ta yana k**a da na gyada, da na filasko.
BANGARORIN DA AKE MAGANI DA SHI A JIKIN TA
(PART OF USES):
Bangaren da ake amfani da shi a jikinta su ne: Baki-dayan ta, k**ar:-
Hudar, Ganye, 'Ya'ya da kuma, Saiwa.
Ko shakka babu Mangungunan da ake yi da Tafasa, ko in ce; Amfanin da Tafasa ke da shi wajen magani yana da yawa, wani Karin-magana da Hausawa ke yi wato: (Da Magani a gonar yaro).
GANYEN TAFASA (LEAFS):
Ganyen Tafasa yana maganin:
*Zazzabi, (fever).
* Murar-kirji, (Neumonia),
*Matsalar Maqogaro (thoracic ),
*Sanyin-kashi mai riqe guiwa (Artritis), *Magance Tari (cough), kuma Yana
*Maganin Mantuwa.
'YA'YAN TAFASA (Seeds):
'Ya'yan Tafasa yana magance:
*Cututtukan fata, (Antidermatitis/skin diseases),
*Macijin-ciki,
*Tsutsar-ciki,
*Rage radadin cutar (HIV) (huma immune virus),
*Ciwon kumburi, kuma yana
*Maganin Tarin-Tibi
SAIWAR TAFASA (Root):
Sawar Tafasa tana maganice:-
*Matsalar toshewar Mafitsara,
*Matsalar tsiro ko fitar ciwo a Mafitsarar Mace (Cystitis),
*Qaban- ko karine-Mahaifa (fibroid),
* Kumburin magudanar fitsari (prostate), ga Maza,
*Cizon maciji. Da sauransu
KADAN DAGA SINADARAN DA TAFASA TA QUNSA
Tafasa ta qunshi Sinadarai k**ar haka:
*Linoleic acid,
*Palmitic acid,
*Oleic acid da kuma
*Protein. Da sauransu
FA'IDA:
'Ya'yan Tafasa idan aka Soya su, aka dake su, aka mai da su gari, sai akwaba da zuma a dinga shan karamin cokali safe da yamma tsawon kwanaki bakwai, to, wannan hadin yana maganin abubuwa k**ar haka;-
*Kurajen sanyi,
*Ciwon mara na mata. da
*Warin qashi. Idan an haxa da Kanimfari da Citta.
Da sauran su.
Dr. Yakubu Maigida Kachako.Shatiman Kachako/Jarman Daho