25/08/2026
GIDAUNIYAR ALBASAR INTERNATIONALFOUNDATION DA CHRISTOFFEL BLINDEN MISSION SUN KADDAMAR DA WANI SHIRI NA SHEKARU HUƊU A YANKIN TAHOUA NA JUMHURIYAR NIJAR
Shirin zai samar da tiyatar ido sama da 3,000, horar da ma’aikatan lafiya 60 tare da samar da kayan aiki ga Asibitin Yankin Tahoua
Tahoua, Jamhuriyar Nijar — A yau ne aka ƙaddamar da wani babban shirin kula da lafiyar ido karkashin gidauniyar Albasar InternationalFoundation da kuma Chrispffel Blinden Mission a yankin Tahoua na Jamhuriyar Nijar, wanda aka tsara domin ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar ido da kuma rage matsalar makanta da za a iya kauce mata a yankin.
Shirin, wanda zai gudana na tsawon shekaru huɗu, zai mayar da hankali wajen samar da damar samun ingantaccen kulawar ido ga al’ummomin da ke yankunan Tahoua, Madaoua da Konni.
A ƙarƙashin shirin, an tsara gudanar da tiyatar ido sama da 3,000 ga mutanen da ke buƙatar magani da tiyata domin dawo musu da gani.
Baya ga aikin tiyata, shirin zai kuma mayar da hankali wajen gina ƙwarewar ma’aikatan lafiya na cikin gida, inda za a horar da akalla ma’aikatan lafiya 60 domin ƙara musu ilimi da ƙwarewa wajen gano matsalolin ido, kula da marasa lafiya da kuma samar da ayyukan kula da lafiyar ido mai ɗorewa.
Wani muhimmin ɓangare na shirin shi ne ƙarfafa da samar da kayan aikin da ake buƙata a Asibitin Ido na Makkah da ke Yankin Tahoua, domin inganta ayyukan kula da lafiyar ido da kuma tabbatar da cewa al’ummar yankin za su ci gaba da samun ingantattun ayyukan lafiya ko bayan kammala shirin.
Gina tsarin kula da lafiyar ido mai ɗorewa
Shirin Albasar da CBM ba zai tsaya ne kawai kan gudanar da tiyata ba. Manufarsa ita ce ƙarfafa tsarin kula da lafiyar ido ta hanyar samar da magani, horar da ma’aikata, samar da kayan aiki da kuma inganta tsarin lafiya na cikin gida.
Ta wannan hanya, ana sa ran shirin zai taimaka wajen kawo ayyukan kula da lafiyar ido kusa da al’umma, musamman waɗanda ke fuskantar matsalar rashin samun isasshen kulawar ido.
Ayyukan za su kuma haɗa da wayar da kan jama’a game da muhimmancin duba ido da wuri, gano cututtukan ido tun kafin su yi tsanani, da kuma tura marasa lafiya zuwa wuraren da za su samu kulawar da ta dace.
A cewar masu gudanar da shirin, manufar Albasar da CBM ita ce samar da tasiri mai ɗorewa a fannin lafiyar ido a yankin Tahoua da sauran wuraren da shirin ya shafa.
Tare da gudanar da dubban tiyatar ido, horar da ma’aikatan lafiya da kuma ƙarfafa Asibitin Yankin Tahoua da kayan aiki, ana sa ran shirin zai taimaka wajen ƙara yawan mutanen da za su samu damar samun kulawar ido cikin sauƙi da wuri.
Shirin ya kuma ƙara jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin agaji, hukumomin lafiya da cibiyoyin kula da lafiya wajen yaƙi da matsalar makanta da za a iya kauce mata.
Albasar International Foundation na ci gaba da ƙoƙarinta wajen tallafawa ayyukan kula da lafiyar ido da kuma taimakawa al’umma wajen samun damar yin magani, tare da manufar samar da makoma mai kyau ga mutanen da ke fama da matsalolin gani.
Ƙaddamar da wannan shiri na Albasar daCB a Tahoua na wakiltar wani muhimmin mataki wajen cimma wannan buri, tare da fata cewa cikin shekaru huɗu masu zuwa, dubban mutane za su amfana da ayyukan shirin, yayin da tsarin kula da lafiyar ido a yankin zai ƙara ƙarfi da ɗorewa.
Albasar International Foundation — Domin Idanu Masu Ganin Bege