05/02/2026
SANARWA TA MUSAMMAN GA AL’UMMAR MUSULMI
(Ramadan Food Distribution Committee.)
A ci gaba da ayyukan alkhairi da Kungiyar FITYANUL ISLAM OF NIGERIA ke gudanarwa a watan azumi, Moduganari Detachment, MMC LG – Borno State Branch, na sanar da al’ummar Musulmi masu kishin addini da aikin alkhairi cewa, kamar yadda aka saba duk shekara, kungiyar ta fara shirye-shiryen tallafa wa marasa ƙarfi a cikin watan azumin Ramadan.
A wannan shiri, ana raba abubuwan bude baki kamar kunu/kosai, dabino, ruwa, da sauran kayan abinci domin sauƙaƙa wa marasa galihu da masu ƙaramin ƙarfi yayin Buda Baki a azumi.
Saboda haka, muna kira ga dukkanin yan’uwa Musulmi mai hali da ya saka hannun jari tare da bada gudummuwa gwargwadon iko, domin samun falalar wannan aikin Alkhairi a wajen Allah (SWT) a cikin watan RAMADAN. Wanda ya taimaka yau, Allah zai ninka masa lada sau da dama, Allah ya Bada ikon taimakawa Amin.
Muna karɓar gudummuwa iri-iri, ciki har da:
– Kuɗi,
– Ruwan fiyawata,
– Hatsi na kunu,
– Suga,
– Gyada,
– Leda,
– Itace ko gawayi,
– Mai ko manja,
– Wake,
– Da sauran kayayyakin tallafi.
Daga cikin abubuwan da aka lissafo, duk wanda aka samu daga cikinsu muna matuƙar buƙata, kuma za a karɓe su hannu bibbiyu.
Akwai lambar asusu (Account Number)
👇👇👇
810-348-896-4
Monie Point
Rabiu Babayo
Ga duk wanda yake buƙatar bada gudummuwa, kuma domin ƙarin bayani, a tuntube mu ta lambar waya da ke ƙasa.
👇👇👇
09160626452
08103488964
09016989320
09127507652
Wannan shiri yana gudana ne karkashin tutar FIRST AID GROUP FITYANUL ISLAM OF NIGERIA, BORNO STATE BRANCH, MMC LG – MODUGANARI DETACHMENT, karkashin jagorancin Capt. Rabiu Babayo, Chairman, Ramadan Food Distribution Committee.
🙏Allah Ya karɓi gudummuwarmu, Ya sa ta zama sanadiyyar samun rahama da gafara. Ameen 🤲🏽
✍️ Rabiu Babayo
BORNO MEDIA TEAM