AREWA A YAU

AREWA A YAU El mago 🪃

Buni ya sasanta Yahaya Bello da Ajaka, Bellon ya ce “kuskure ɗabi’ar ɗan'adam ce, yafiya kuma ta Ubangiji”Shugaban Kwami...
07/05/2026

Buni ya sasanta Yahaya Bello da Ajaka, Bellon ya ce “kuskure ɗabi’ar ɗan'adam ce, yafiya kuma ta Ubangiji”

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa don sasanta rikicin cikin gida na APC, kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya sasanta tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023 a jihar Kogi, Murtala Yakubu Ajaka.

Mai Mala Buni, wanda ya raka Ajaka zuwa gidsn Yahaya Bello da ke Abuja, ya bayyana Bello a matsayin tsohon aboki, ɗan’uwa kuma jajirtaccen ɗan jam’iyya, yayin da ya ce Ajaka ma amintaccen abokin aiki ne. Buni ya jaddada cewa duk wata saɓani dole ne ta ƙare da sulhu, yana mai cewa a matsayinsu na ‘yan APC, wajibi ne su warware saɓanin da ke tsakaninsu tare da aiki tare.

“Dukkanmu mun san cewa kowace gardama tana da ƙarshe. Mun yi shekaru muna aiki a matsayin ‘yan’uwa, kuma duk abin da ya faru a zaɓen da ya gabata ya kamata a bar shi a baya yanzu. Mai girma Yahaya Bello, Ajaka ɗan’uwanka ne, kuma na san ku sosai. Wannan rabuwar ba za ta ci gaba ba. Kamar yadda na tattauna da kai, tare za mu samu ci gaba. Ina gode maka bisa wannan sulhu na yau. Ina kuma gode wa dukkan mambobin kwamitin sulhu, musamman Alhaji Ibrahim Masari” in ji shi.

Da yake mayar da martani, Yahaya Bello ya gode wa gwamnan jihar Yobe da mambobin Kwamitin Tsare-tsare, Sasanta Rikice-rikice da Wayar da Kai na APC bisa rawar da s**a taka wajen sasanta shi da Ajaka.

“Da farko ina gode wa Allah, sannan ɗan’uwana gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni. Ina matuƙar godiya gare ka. Haka kuma ina gode wa Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Masari, Wazirin Katsina, bisa gudunmawar da ya bayar da kuma yadda ya riƙa tuntuɓata kan wannan batu.

“Mutane da dama sun ƙira ni tare da ganawa da ni a madadin ɗan’uwana Yakubu, suna roƙona da in yafe masa bisa duk wani kuskure da ya yi. A wannan yammaci, na nuna masa inda ya yi kuskure ta fuskar siyasa, al’ada da sauran fannoni, kuma ya amince da kuskurensa. A yau na karɓe shi cikin iyal

Aisha Binani ta kai ziyarar ta'aziyya gidan Hon. A. A. Zaura da ke Kano domin yi masa ta'aziyya bi rasuwan mahaifinsa.
07/05/2026

Aisha Binani ta kai ziyarar ta'aziyya gidan Hon. A. A. Zaura da ke Kano domin yi masa ta'aziyya bi rasuwan mahaifinsa.

Ba za a dawo da tallafin man fetur a Nijeriya ba - Gwamnatin TarayyaMinistan Kudi da kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiw...
06/05/2026

Ba za a dawo da tallafin man fetur a Nijeriya ba - Gwamnatin Tarayya

Ministan Kudi da kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, duk da ƙorafe-ƙorafen da ake yi kan tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Paris na ƙasar Paris, inda shi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu s**a gana da masu zuba jari na duniya.

Oyedele ya ce tallafin na haifar da nakasu a tattalin arziki, yana mai cewa ba za a kayyade farashin fetur ba, domin gwamnatin na ganin kasuwa za ta iya daidaita kanta.

06/05/2026

With Fagen wasannin kwallon kafa – I just got recognized as one of their top fans!

Hamidu Yace, Ni Gaskiya Kindameni, In Zaki Iya Zama Dani Ahaka Kizauna Dani, Inkuma Bazaki Iya Zama Dani Ahaka Bah, Zans...
04/05/2026

Hamidu Yace, Ni Gaskiya Kindameni, In Zaki Iya Zama Dani Ahaka Kizauna Dani, Inkuma Bazaki Iya Zama Dani Ahaka Bah, Zansauwake Miki Kitafi Can Ki Auri Liman Koh Ladan, Yauwa, Ni Nagaji Gaskiya Haba Haba Haba Da'Allah!!! Saikace Ni Jikan Limamin Saudiyya Ne Ni, Mutum Ace Kata Sallah

Dukfah Wannan Hayaniyyar AKan Yayi Sallah Fah, Lalle Maimuna Kina Cikin Lukutar KADDARA

Abdul Amart Kada Ku Daurawa Maimuna Depression, Domin Zamu Iya Karar Ku!😆

Maimuna tana ganin rayuwa, domin ta rabu da mai kishi tsinya da zargi, an fada gurin marar sallah da neman mata.

KADDARA Shiri ne mai cike da darasi, nishadi da sakonni masu tasiri da zasu taba zuciyarku.

Kuci gaba da kallon shirin KADDARA

Kwankwaso: Dila, Sarkin Wayo!Ra'ayin Elyahya BichiRabiu Musa Kwankwaso yana da cikakkiyar masaniya cewa, ko a wace jam’i...
04/05/2026

Kwankwaso: Dila, Sarkin Wayo!

Ra'ayin Elyahya Bichi

Rabiu Musa Kwankwaso yana da cikakkiyar masaniya cewa, ko a wace jam’iyya Peter Obi ya tsaya takara, ba zai samu cikakkiyar karɓuwa a wurin mutanen Arewa ba.

Sai dai kuma, ba burin Kwankwaso ba ne ganin Peter Obi ya yi nasara. A maimakon haka, ana ganin yana iya goyon bayan Obi tare da amincewa ya zama mataimakinsa domin cimma wasu manufofi guda uku kamar haka:

Na farko: Tsayawa takara a matsayin mataimaki ga Peter Obi na iya buɗe masa ƙofa zuwa yankin Kudu maso Gabas (yankin Ibo). Wannan zai ba shi damar ƙulla sabbin alaƙa da manyan ‘yan siyasa a yankin, tare da samun karɓuwa a wajen talakawa—abin da zai zame masa jari a siyasar gaba.

Na biyu: Kwankwaso na iya amfani da wannan damar wajen yi wa Peter Obi abin da Hausawa ke kira “angiza mai kantu ruwa.” Wato idan Obi ya sake tsayawa takara a 2027 kuma ya faɗi, hakan zai rage masa tasiri sosai. A irin wannan yanayi, zai yi wuya ya sake tsayawa a 2031, musamman idan aka koma tsarin dawo da mulki zuwa Arewa. A ƙarshe, hakan na iya tilasta masa ya koma mai mara wa Kwankwaso baya.

Na uku: Rarrabuwar kan jam’iyyun adawa na iya rage yawan kuri’un da Atiku Abubakar zai samu. Haka kuma, ana ganin cewa wannan na iya zama karo na ƙarshe da zai samu damar tsayawa takara.

Idan wannan lissafi na Kwankwaso ya tabbata, zuwa 2031, lokacin da ake tsammanin mulki zai dawo Arewa, zai iya fitowa a matsayin babban jigo mai rinjaye, yana mai kallon kansa a matsayin mafi cancanta da tikitin shugaban ƙasa daga yankin.

Sai dai kuma, abin da ake ganin kamar yana mantawa da shi shi ne: bayan Atiku, akwai wasu ‘yan siyasa masu tasowa a Arewa. Daga cikinsu akwai Nasir El-Rufai, wanda gogewarsa a mulki da faɗin alaƙarsa a faɗin ƙasa na iya sanya shi zama babban ɗan takara a 2031.

Bugu da ƙari, daga Arewa maso Gabas akwai Kashim Shettima, wanda shi ma zai iya nuna sha’awar neman kujerar shugaban ƙasa a lokacin.

A ƙarshe, tambayar ita ce: shin wannan lissafi na Kwankwaso zai kai ga nasar

Labari Da Ɗumi-Ɗuminsa: Atiku zai tafi Amurka domin kai ƙaran Tinubu ga ƙasashen duniyaTsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa a...
03/05/2026

Labari Da Ɗumi-Ɗuminsa: Atiku zai tafi Amurka domin kai ƙaran Tinubu ga ƙasashen duniya

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya kuma madugun ƴan adawan ƙasar, Atiku Abubakar ya tabbatar da shirin tafiyarsa zuwa ƙasar Amurka domin jawo hankalin ƙasashen duniya kan matsalolin tsaro, tsadar rayuwa da kuma raguwar ingancin shugabanci a Najeriya.

A yayin ziyarar tasa, Atiku zai gana da masu tsara manufofi da manyan cibiyoyi a Amurka domin tattauna halin da ƙasar ke ciki.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar “babban rikicin cikin gida” wanda ba za a iya raina shi ko siyasantar da shi ba.

Ya ce daga rikice-rikicen da ke addabar Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, zuwa zubar da jini a yankin Middle Belt, da kuma ƙaruwar sace-sacen mutane da aikata laifuka a faɗin ƙasar, duk na nuna cewa gwamnati na rasa ikon kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A cewarsa, lamarin ya wuce na ɗaiɗaikun hare-hare zuwa wata babbar matsala ta gazawar tsarin tsaro, inda al’ummomi ke lalacewa, hanyoyin rayuwa ke durƙushewa, kuma ‘yan ƙasa ke fuskantar halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

A cikin mintuna 33 Inter Miami ta zazzagawa Orlando City kwallaye har uku, Messi na farin ciki sosai a lokacin domin shi...
03/05/2026

A cikin mintuna 33 Inter Miami ta zazzagawa Orlando City kwallaye har uku, Messi na farin ciki sosai a lokacin domin shine ya zura ta ukun. Amma sai wasan ya sauya, Inter ta fara dibar kaya har Orlando tayi come-back kuma ta basu kashi. Har yanzu Inter Miami bata samu nasara ko daya ba a sabon filin wasanta bayan buga wasani masu yawa.

Cristiano Ronaldo ya girmi Higuain da Roony, amma yanzu idan ka kalli hotunansu zaka ce sune s**a girme shi sakamakon gi...
03/05/2026

Cristiano Ronaldo ya girmi Higuain da Roony, amma yanzu idan ka kalli hotunansu zaka ce sune s**a girme shi sakamakon gin jikinsa da yake yi ba dare ba rana. Kuma har yanzu yana taka leda a babban mataki.

Labari Da Ɗumi-ƊuminsaPeter Obi ya tabbatar da shirin ficewarsa daga jam’iyyar ADC, inda ya alaƙanta matakin da rikice-r...
03/05/2026

Labari Da Ɗumi-Ɗuminsa

Peter Obi ya tabbatar da shirin ficewarsa daga jam’iyyar ADC, inda ya alaƙanta matakin da rikice-rikicen cikin gida, zargin rarrabuwar kai, da kuma shari’o’in da ke gaban kotu da s**a dabaibaye jam’iyyar, kamar yadda yake s cikin wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi.

02/05/2026

Address

Seb
Mubi
650

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA A YAU posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share