10/12/2025
Kidney failure (also called renal failure) na lokacin da koda ta daina aiki yadda ya kamata. Kodan mutum suna da ayyuka uku masu muhimmanci:
1. Tsarkake jini – su cire datti da gubobi daga jini.
2. Sarrafa ruwa da gishiri a jiki.
3. Taimakawa da matsa lamba da ƙirƙirar wasu sinadaran jiki.
Idan koda ta fara lalacewa sosai, ba za ta iya yin waɗannan ayyuka ba — wannan ake kira kidney failure.
Nau’o’in Kidney Failure
1. Acute kidney failure (akwai na gaggawa)
– Yana faruwa cikin sauri (kwanaki ko makonni).
– Yawanci sakamakon rashin ruwa, jini ya rasa gudu, magunguna masu haɗari, ko cuta mai tsanani.
– Yakan warke idan an gano da wuri.
2. Chronic kidney failure (na É—an lokaci/tsawon lokaci)
– Yana faruwa a hankali cikin shekaru.
– Yawanci sakamakon hawan jini ko sukari (diabetes) da ba a kula da su ba.
– Yana iya kaiwa ga buƙatar dialysis ko dashe koda (transplant).
Manyan Alamomin Kidney Failure
Kasala sosai
Kumburin ƙafa, idanu ko fuska
Rage yin fitsari ko yawan yin fitsari da dare
Fitsari mai kumfa
Ciwon gefe ko ƙugu
Ama’i, rashin ci
Hawan jini da ke ƙaruwa
Manyan Abubuwan da ke Jawo Kidney Failure
Hawan jini (hypertension)
Ciwon sikari (diabetes)
Rashin ruwa sosai
Magunguna masu cutar da koda (NSAIDs kamar ibuprofen, diclofenac)
Infection
Blockage a mafitsara (stones, prostate, da sauransu)
Yadda ake Magani
Idan na gaggawa ne: a gyara dalili (kamar rage drug, ƙara ruwa, magance infection).
Idan na tsawon lokaci ne:
Kula da hawan jini da sikari
Rage gishiri
Gujewa magungunan da ke cutar da koda
Diet na kidney
Dialysis idan koda ta daina aiki sosai