Sirrin Rayuwar Aure

  • Home
  • Sirrin Rayuwar Aure
Call Website

Sirrin Rayuwar Aure we're passionate about marriage awareness, relationship education, and helping people build stronger relationships.
(2)

Dedicated to sharing knowledge, solving marital challenges, and inspiring positive change through meaningful, educative, and entertainment.

A shekara 2015 Gani nake idan 2020 tayi banyi aure ba nikam na hakura da aure 🤣 toh mai zan zauna jira shekara 5 fa, kai...
05/10/2026

A shekara 2015 Gani nake idan 2020 tayi banyi aure ba nikam na hakura da aure 🤣 toh mai zan zauna jira shekara 5 fa, kai ina bazan iya ba.😄 Sai gani a 2026 😭

ban mutu ba kuma banyi auren ba. kana taka Allah yana nashi. Allah ubangiji ya shiga lamuran mu baki daya 🙏

05/10/2026

Wacce unguwa ne duk jihar da kaje akwai ta??

05/10/2026

Sunana Ruma Shekaruna 22 Babu aure

😩💔😭

Malama Ban taɓa ganin Masifa irin wannan ba.Matata na k**a tana chatting da ƙanina uwa ɗaya uba ɗaya , ta tuttura masa h...
04/10/2026

Malama Ban taɓa ganin Masifa irin wannan ba.

Matata na k**a tana chatting da ƙanina uwa ɗaya uba ɗaya , ta tuttura masa hotunan sassan jikinta.

Har suna maganar haɗuwarsu ta rannan ta bada citta.

Bana taɓa mata waya tsautsayi jiya aka Turo msg tana ɗaki tana Sallah wayar tana kusa dani akan tv stand na dakko ban buɗe wayar ba sai daga saman screen naga an rubuta LULUNA shine yaja hankalina na danna msg ɗin sai naga ana cewa masoyiya na tura sako ta whatsap.

Naje whatsap zan duba an saka wa whatsap din Madannan sirri , na saka date of birth ɗinta cikin mamaki sai ya bude.

Sai ko naga sakonnin da s**a shigo daga LULUNA sune sakonnin sama abinda ya kiɗima ni Yaddah naga hotunan ƙanina da nata kala kala, wasu ta tura masa wani ya Turo mata , wasu suna tare , nayi maza nayi screen shoot na tuttura wayata har da vedios da suke tare na tuttura .
Nagoge k**ar ban gani ba.

Har yanzu ban nuna mata na gani ba na rasa ta ina zan fara .

Ko kallanta na kasa yi.
Tana ta tambaya ta lfy ina ce mata ba komai.

Ya zanyi Malama .
Don banjin zan iya zama da ita .

UMMA SULEINAN 😭

ILLAR RASHIN GAMSAR DA MACE A LOKACIN JÍM@'IA cikin aure, kusancin ma'aurata ba wai kawai wata bukata ce ta jiki ba; yan...
04/10/2026

ILLAR RASHIN GAMSAR DA MACE A LOKACIN JÍM@'I

A cikin aure, kusancin ma'aurata ba wai kawai wata bukata ce ta jiki ba; yana kuma da alaka da soyayya, kusanci, fahimtar juna da kwanciyar hankali a tsakanin ma'aurata. Saboda haka, idan mace tana yawan jin cewa ba a kula da bukatunta yayin kusancin aure, hakan na iya haifar da matsaloli da dama a cikin dangantaka.

1. ZAI IYA HAIFAR DA DAMUWA DA RASHIN JIN DADIN AURE

Idan mace tana jin cewa kullum ana kula ne da bukatar namiji kawai, ba tare da an tambayi abin da ita ma take bukata ba, tana iya fara jin k**ar ba a damu da ita ba. Wannan na iya rage farin cikinta da kusancin da take ji da mijinta.

2. ZAI IYA RAGE SHA'AWAR MACE

Rashin gamsuwa akai-akai na iya sa mace ta fara guje wa kusancin aure ko kuma sha'awarta ta ragu. Amma ya k**ata a fahimci cewa rashin sha'awa ba koyaushe yana nufin mijin ne kadai yake da matsala ba; damuwa, rashin lafiya, canjin hormones, wasu magunguna, matsalolin aure da sauran abubuwa na iya shafar sha'awar mace.

3. ZAI IYA HAIFAR DA NISANTAR JUNA

Idan ba a tattauna matsalar ba, mace na iya fara boye abin da take ji. Daga nan sai kusancin zuciya ya fara raguwa, domin tana iya jin cewa ba a fahimce ta ko kuma ba a saurare ta.

4. ZAI IYA HAIFAR DA RASHIN FAHIMTAR JUNA

Wasu ma'aurata suna tunanin cewa dole ne abokin aure ya san abin da ɗayan yake so ba tare da an fada masa ba. Wannan ba koyaushe yake faruwa ba. Bukatun mutane sun bambanta, kuma abin da yake faranta wa mace ɗaya rai ba lallai ne ya kasance haka ga wata ba. Saboda haka, magana cikin mutunci da sauraron juna yana da muhimmanci.

5. ZAI IYA SHAFAR AMINCI DA SOYAYYA

Idan matsalar ta dade ba tare da an magance ta ba, tana iya haifar da fushi, takaici ko jin an yi watsi da ita. Idan aka bar irin wannan yanayi ya yi tsawo, zai iya shafar yadda ma'aurata suke kallon juna.

TO ME YA KAMATA MA'AURATA SU YI?

Abu na farko shi ne sadarwa. Miji ya k**ata ya iya tambayar matarsa cikin mutunci abin da take so da abin da ba ta jin dadi da shi. Haka ita ma mace ta k**ata ta bayyana bukatunta ba tare da kunya ko zargi ba.

Kada a mayar da kusancin aure k**ar gasa ce ta ganin wanda zai fi samun abin da yake so. Abin da ya fi muhimmanci shi ne ma'aurata su kula da jin dadin juna, su kasance masu hakuri, tausayi da fahimtar juna.

Haka kuma, ba dole ne gamsuwar mace ta kasance daidai da kaiwa ga inzali ba a kowane lokaci. Wasu mata suna bukatar karin lokaci da yanayi na kwanciyar hankali kafin su samu cikakkiyar sha'awa ko jin dadi. Kuma wasu mata ba sa samun inzali daga shigar azzakari cikin farji kadai; irin yadda jikin mace yake amsawa ya bambanta daga mutum zuwa mutum.

Idan mace tana fama da ciwo yayin jima'i, bushewar farji, rashin sha'awa mai dorewa ko matsalar inzali, bai k**ata a dauki lamarin da wasa ba. Wadannan matsalolin na iya samun dalilai na lafiya, hormones, damuwa ko wasu matsalolin dangantaka, kuma ana iya samun taimakon kwararrun ma'aikatan lafiya.

Don haka:

Mace ba kayan biyan bukata ba ce, namiji ma ba haka yake ba. Auren da yake da karfi yana bukatar soyayya, sadarwa, mutunta juna, fahimtar juna da kula da bukatun juna.

Idan kana son kyakkyawar rayuwar aure, kada ka tambayi kanka kawai: “Na gamsu?” Ka kuma tambayi abokin zamanka: “Ke kina jin dadi? Akwai abin da zan gyara?”

Wannan karamar magana ce, amma tana iya bude kofar babban sauyi a rayuwar aure.

Sirrin Rayuwar Aure Backup

04/10/2026

kokasan meyasa mata s**afi Maza kwarjini ?

03/10/2026

Dan allah Idan kasan ba auranta zakayi ba, Dan Allah karabu da yarinyar mutane tanimi mijin aure.

Sati daya kenan bama magana da kanina. To jiya yazo gida da kaza cikin leda irin waɗanda ake sayarwa figaggu. Ya ɗora ka...
03/10/2026

Sati daya kenan bama magana da kanina. To jiya yazo gida da kaza cikin leda irin waɗanda ake sayarwa figaggu. Ya ɗora kaza a tukunya zai fara girki kenan, sai kila ya tuna bai siyo kayan miya ba, ko ya akayi oho.

Fitarsa ke da wuya, yan sanda s**a k**a shi. Sai bayan sallar la'asar aka sake shi.

Da ya dawo gida, kazar ta gaji da dahuwa ta koma gawayi saboda ba kowa a gidan. Ni kawai ce kishiyar mamanmu. Kuma duk baya yi mana magana. Don ma akan electric ne da Gas ne, da sai mu fita mu bar gidan saboda fashewa zai yi.

03/10/2026

jama'a wai ya akeso mutum yayine 20yrs wai Amma har anfara mgnn kaqi kayi aure waidama ana haka 😭😭

02/10/2026

Meyasa bayan Aure mata kiyen kiba shi kuma miji ya rame?

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sirrin Rayuwar Aure posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your practice to be the top-listed clinic?

Share