Taska

Taska Dubban Hanyoyi na Dabarun saukake Fahimtar rayuwa.

Ta ganni da IPhone sai ta yi sauri ta matso ta ce Malam don Allah ka ɗan ɗaukeni hoto da wayanka….  Na ce a nawa ? Ta ce...
25/08/2026

Ta ganni da IPhone sai ta yi sauri ta matso ta ce Malam don Allah ka ɗan ɗaukeni hoto da wayanka…. Na ce a nawa ? Ta ce zan baka numberna sai ka turamin ta wasap.

Na ce ok to na gane.

To na amshi number amma wannan hoto kam sai dai ta ɗaukeshi a ta Facebook don na yi saving number amma na manta me na rubuta 🤣

Shekarunta sha tara amma ta sayuwar ɗaukar hoto 🤔 kai nisa’u ba su ji 🥲

A lokacin da zan yi aure;A wannan watan zan roki dukkan matan Najeriya ta dukkan hanhoyi da sakona zai iya isa birni da ...
24/08/2026

A lokacin da zan yi aure;
A wannan watan zan roki dukkan matan Najeriya ta dukkan hanhoyi da sakona zai iya isa birni da ƙauye cewa don Allah don Ma’aiki kada wacce ta ɗauki ciki a wannan watan.

Saboda ina so ya kasance a watan da zan haifi farkon yarona yq zamana a kaf Najeriya babu wani haihuwa da za a yi sai a gidana.

Kuma inshaAllah zan sami hadinkai daga gareku

Ba a cikin son raina ba yau zan tona wa Hausawa Asiri, fulani su yi musu dariya. 😁Duk wata yar Bahaushe da ka ga gashi y...
23/08/2026

Ba a cikin son raina ba yau zan tona wa Hausawa Asiri, fulani su yi musu dariya. 😁

Duk wata yar Bahaushe da ka ga gashi ya yi bindi ta baya to ba gashinta bane, ga abin da suke sawa nan….

Bincike ya nuna babu Bahaushiyar da gashinta yake sauka har kafaɗa, gashi har kafaɗa sai fulanin jikokin Usmanu ɗan hodiyo 👌🏾

Ni fa ba zan taɓa zuwa aikin haji ba sai na tabbatar da:-- Ina da abicin shekara a ajiye!- Ina da gida da mota da tsayay...
22/08/2026

Ni fa ba zan taɓa zuwa aikin haji ba sai na tabbatar da:-

- Ina da abicin shekara a ajiye!
- Ina da gida da mota da tsayayyen sana’a!
- Dukkan dangina ba wanda ake binshi bashi!
- Dukkan dangina babu wanda ya rasa abin da zai ci a kalla na wata daya a ajiye!!!

Idan ba su cika ba to ba zan zuba dukiyana a hawa jirgi ba.
Ko an biya min ba zan je ba sai komai ya yi daidai.

Yanzu Hatta ɗan yanke farcen da mata suke yi da kansu a cikin ɗakinsu sun fara gajiya da shi suna neman masu yankan farc...
21/08/2026

Yanzu Hatta ɗan yanke farcen da mata suke yi da kansu a cikin ɗakinsu sun fara gajiya da shi suna neman masu yankan farce a waje.

Ina tunanin saboda ayyukan gida ne da s**a yi musu yawa - tun daga wanka, wanki, wanke-wanke, girki, shara har zuwa kula da yara da ma lokacin shiga yanar gizo (special media) sannan ga rashin bacci tunda miji zaizo da daddare ya hanasu numfashi ballantana har su sami damar yin minshari.

Amma duk da haka wasu suna ganin gara matan su zauna a cikin gida ta yadda mai yankan farcen zqi riƙa shiga gida-gida yana rage musu wannan aiki, wasu kuma suna ganin gara matan su riƙa fitowa waje, a yi musu a wannan aiki bainan nasi……

Duk wanda ya san haƙiƙanin inda za a sami mayu masu maita na gasken gaske don Allah ya fada min!!! Wallahi ni ko kaɗan b...
18/08/2026

Duk wanda ya san haƙiƙanin inda za a sami mayu masu maita na gasken gaske don Allah ya fada min!!!

Wallahi ni ko kaɗan ban yarda akwai mayu ko maita ba!

In har an sami inda suke, ko a inane lallai zan je kuma zan nemi su gwada maitan nasu a kaina!!!

Na taba rokon wani da ya ce ya iya yin asiri na ce ya yi min duk abin da zai iya amma unfortunately ba a sami masara ba! Ya bani sati ɗaya na bashi wata ɗaya amma babu natija 😅

Al’adun bikin aure a ƙasar Niger Kamar yadda mata suke zuwa biki da yayansu da jikokinsu, su zauna tun safe har dare a N...
16/08/2026

Al’adun bikin aure a ƙasar Niger

Kamar yadda mata suke zuwa biki da yayansu da jikokinsu, su zauna tun safe har dare a Najeria su yi ta ɗiban girki kala kala, in sun tashi tafiya su kwasa su tafi da shi gida su ci na dare, su ci da safe, to haka ma maza da mata suke yi a ƙasar Nijar amma su maza ba sa ɗiba su tafi da shi in sun tashi tafiya, amma wasu za su iya tafiya su yi wata buƙatar tasu su dawo idan an kawo na rana ko na yamma👌🏾 kamar yadda waau za su iya zuwa da safe daura aure da su su tafi wasu zo da rana, wasu kuma da yamma.

Kuma babu bambanci tsakanin babban birinin kasar da dukkan sassan yankunan ƙasar, ba mai kuɗi ba talaka👌🏾

Akwai zumunci sosai.

Mutane da yawa ba su san cewa a kaf dabbobi babu namar dabba mai kafa uku da ya kai na ƙanduwai dadi ba!
16/08/2026

Mutane da yawa ba su san cewa a kaf dabbobi babu namar dabba mai kafa uku da ya kai na ƙanduwai dadi ba!

Kannena masu pakacity (wato packaging) A kasata Najeriya akwai kowa ya iya packaging, shi ya sa na nake yawan bada fataw...
13/08/2026

Kannena masu pakacity (wato packaging)
A kasata Najeriya akwai kowa ya iya packaging, shi ya sa na nake yawan bada fatawa ga samari akan su daina neman aure daga kawayen amarya ko a ranar sallah🫵🏾

Yau na fito aiki da sassafe sai na ga wata tawaga na uwa da ƴaƴanta biyar suna tafiya sauri-sauri, sai abin ya ja hankal...
12/08/2026

Yau na fito aiki da sassafe sai na ga wata tawaga na uwa da ƴaƴanta biyar suna tafiya sauri-sauri, sai abin ya ja hankalina.
Irin wannan sammakon kuma cikin hanzari haka ina tunanin bara za su tafi…
Bubban damuwana shine: ina uban ƴaƴan yake!? Kuma in ba a yi wasa ba ciki take da shi!!!

Me ye asalin dalilin da ya sa ake yawan samun irin haka a cikin Hausawa?

Rashin karatu da rashin tarbiyya (laifin iyaye!)

Address

Kano
810241

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taska posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Taska:

Shortcuts

Share