18/01/2026
Umar, ɗan uwa ga matar da aka hallaka da ƴaƴanta shida, ya shiga hannun Ƴansanda tare da wasu mutum biyu a Dorayi Chiranchi.
Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta sanar da cafke mutum uku da ake zargi uku da shirya tare da aiwatar da kisan gilla da aka yi wa wata matar aure da ƴaƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi a ranar 17 ga Janairu, 2026.
Kakakin Ƴansandan Jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an samu nasarar cafke mutanen ne bisa umarnin Sufeto Janar na Ƴansanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, inda aka yi amfani da dabarun aikin tsaro na leƙen asiri.
Kiyawa, ya ce aikin kamen ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƴansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, tare da tawagar kwararrun jami’ai.
A cewarsa waɗanda aka cafke sun hada da Umar Auwalu, mai shekaru 23 daga Sabuwar Gandu; Isyaku Yakubu, wanda aka fi sani da Chebe, mai shekaru 40 daga Sagagi; da kuma Yakubu Abdulaziz, wanda ake kira Wawo, mai shekaru 21 daga Sabon Gida Sharada.
Ƴansanda sun ce an cafke su ne a wani sumame da ya gudana daga karfe 10 na dare ranar 17 ga Janairu zuwa karfe 4 na asuba ranar 18 ga Janairu, 2026.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa Umar Auwalu, wanda ake zargin shi ne shugaban kungiyar kuma dan uwa ga marigayiyar, ya amsa laifin aikata kisan. Ya kara da cewa wanda ake zargin ya bayyana wa Ƴansanda cewa su ne s**a aikata wasu hare-hare da kashe-kashe a baya-bayan nan a wasu unguwannin Kano, ciki har da wani lamari a Tudun Yola.
Ƴansandan Jihar Kano sun ce an kwato kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin, ciki har da wasu tufafi masu dauke da tabon jini, wayoyin salula guda biyu na marigayiyar, adda, gora, da kuma wasu kudade da ake zargin an kwace a wurin da abin ya faru. Bincike na ci gaba domin gano karin bayanai da sauran wadanda ka iya hannu a lamarin