In-Charge in Office

Call Directions Contact the practice

In-Charge in Office This page it's a good and wonderful page,it helps people to get the medical care from Malam Auwal.

Baya Goya marayu, mai uwar ka goyashi.Alhaji Salisu Kantin Sauki Dallatun Bakundi, Allah kara sutura. Wurinka shine gani...
29/01/2024

Baya Goya marayu, mai uwar ka goyashi.
Alhaji Salisu Kantin Sauki Dallatun Bakundi, Allah kara sutura.
Wurinka shine ganin kowa cikin farin ciki da walwala.
Muna Alfahri da kai a dadin garin Bali dama Jahar Taraba baki daya, ta wurin kyautatawa mai karamin karfi, musamman idan kazo Sayan kaya a wurin sa ya kan sauwaka fiye da yadda yasa farashi.
Idan kazo zaka tabbatar da haka, Allah ya kara wadata da daukaka, Allah ya kara Kare mana kai daga dukkan abin ki sirrin Wa jahran.
🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲

ILIMI BA,A KARYARSA, KUL HAATU BURHANUKUM INKUNTUM SADIQIN.Allah ya kara Kare gaskiya a duk inda take.Mu Leƙa Mu GanoFat...
20/01/2024

ILIMI BA,A KARYARSA, KUL HAATU BURHANUKUM INKUNTUM SADIQIN.

Allah ya kara Kare gaskiya a duk inda take.

Mu Leƙa Mu Gano
Fatawar Maulana Prof. MAQARI...

Bayan da na ga faifan na yawo, a matsayina na ɗalibin ilimi sai na duƙufa binciken gano haƙiƙanin fatawar. Shin son zuciya ne ko kuwa baje Kolin ilimi ne?
Sai na samu ilimi ne tsagwaro, amma yana da ɗan nisa. Ga abin da na gani:

(كَالْمَرْأَةِ لَا تَجِدُ مَنْ يَسُدُّ رَمَقَهَا إلَّا لِمَنْ يَزْنِي بِهَا) سَحْنُونَ: وَأَمَّا الْمَرْأَةُ تَخَافُ عَلَى نَفْسِهَا الْهَلَاكَ مِنْ الْجُوعِ وَلَا تَجِدُ مَنْ يَسُدُّ رَمَقَهَا إلَّا لِمَنْ يَطْلُبُ مِنْهَا الزِّنَا فَإِنَّهُ يُسَوَّغُ لَهَا ذَلِكَ لِلْخَوْفِ عَلَى نَفْسِهَا وَيَصِيرُ حَالُهَا حَالَ الْمُكْرَهِ بِتَخْوِيفِ الْقَتْلِ

"K**ar mace ce wadda take jin tsoron rasa ranta saboda yunwa. Sannan ba ta samu wanda zai katange mata wannan buƙatar tata ba, don kar ta halaka, sai dai wanda kawai ya zaɓi ya yi zina da ita sannan ya biya mata buƙatarta, to wannan kam ya halatta gare ta don kawai tsoron rasa rai amma fa. Sai hukuncinta ya zamo kamar wanda aka tilasta ta hanyar barazanar kisa." Imam Sahunun.
Mai neman wannan zance ya leƙa a littafin

تاج الاكليل لمختصر خليل)5/313)
كتاب الطلاق""ألباب الثانى: فى أركان الطلاق"

Ashe Alƙur'ani da ya ba matafiyin da yunwa take neman kashe shi damar cin mushe(matattar dabba) har ma ya yi guzurin da zai raka shi inda jama'a suke, hakan na nufin an buɗe ƙofa a yi ta cin mushe(haram). A wannan gaɓar ma akwai malaman da suke ganin idan mutum ya kuskura yana jin yunwa ya ƙi cin mushe ya ƙi shan wani abin sha har ya mutu, to wuta zai shiga don shi ya kashe kansa.

Ashe da aka halasta mai tsananin buƙata ya shiga gona ko lambu ya ci abin da ke a lambun ba tare da ya yi guzuri ba, nan ma wata ƙofar ce ta sata aka buɗe?

Shahararren Hadisin nan na mutanen da kogon dutse ya rufe da su, inda kowa ya yi tawassali da aikin alkairinsa sannan Allah ya kuɓutar da su. Ɗaya daga cikinsu wanda 'yar uwarsa take ta zuwa neman taimakonsa, shi kuma ya nace ba zai taimake ta a banza ba, sai dai idan ta ba shi kanta sannan, ƙarshe da ta rasa zabi ta bayar da kanta gare shi...(zuwa ƙarshe). Da ma labarin don mu ji mu yi ta mamaki babu wani darasi da za mu koya ciki?

Yadda mutane s**a kalli maganar can a matsayin baƙuwa nan za ka gane akwai aiki ja na neman ilimi musamman gare mu matasa. Yanzu ɗauki misali da ni rabon da in tsuguna gaban malami har na manta. Maganar in saka Uniform in tafi Islamiyya duk da ban girmi litattafan da ake koyarwa ba, tuni na ɗauki hakan matsayin ƙauyanci. Amma yau ni ne nake sanya baki a mas'alar ilimi. Allah mun tuba.

Ba za a rasa sharrin Social media ba. Don masu cewa bai kamata a yada fatawar ba duk da sun yadda gaskiya ce, to sun manta malamin a masallaci ne yake karatunsa tare da masu sha'awar halartar wurin kawai. Waɗanda idan sun ji zancen da ya yi ya rikitar da su, suna da damar neman ƙarin bayani daga gare shi kai tsaye.? To ni fa da nake bibiya ta Social media. Misali kamar mutumin da yake bin jam'in sallah ne amma yana a gida, kawai yana amfani da sautin bututu ne. Idan kayan sauti ya ɗauke ya zai iya kammala sallarsa? Wallahi na gane ba a neman ilimi ta hanyar sauraren audio ko kallon video, sai dai ƙila ana iya ƙara ilimi kawai. Saboda za ka ji maganar da ta yi maka nauyin fahimta, amma ba ka da wani tsani da zai sadar da kai ga mai karatun b***e ka nemi ƙarin bayani. Ihunka banza ke nan! Ƙila shi mai da'awa yana yin karatun gwargwadon fahimtar mutanen da ke gabansa, ba mutanen da ke bibiya daga nesa ba. Yanzu idan ɗalibin firamare ya kamo lecture da ake haskawa Live ta ɗaliban jami'a don Allah me zai hana ya ƙaryata abin da ake faɗa masu na ilimi? Me kuma zai fahimta?

Allah ya jiƙan mazan jiya Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya ce, "Idan Allah ya tashi jarabta ka, sai ya yo ka malami a ƙasar Hausa." Kai ba ka tsira daga malaman ba, marasa ilimin ma ba ka tsira daga gare su ba.

Abin da yake ban mamaki a ƙasar Hausa mun yarda dukkan mai sana'a ko aiki yana iya yin kuskure a aikin sa, amma ban da malami.
Allah ka datar da mu.
Hasali ma babu kuskure a maganar prof. Sai dai neman ina da kuskure kawai daga jahilai.
Kuma abin mamaki shine, yawan cin masu kifar malam da muguwar fahimta babu wanda zai iya kawo wani abu na hujja akan abinda yake fada, sai dai kame - kame kawai.
Dan haka shawara ta a nan Itace abar masu ilimin da maganar ilimin su kawai.

Professor ikon Allah, kaga tasu, taka tayi wuyar gani.

©©© Auwal Ahmed Tsandon Dandela
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️ 19/01/2024

Alhamdu lillah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya hilicce ni ba da sani na ba, kuma ya Rayani ...
15/01/2024

Alhamdu lillah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya hilicce ni ba da sani na ba, kuma ya Rayani ya bani lafiya da arziki ba da wayo na ba.
Yau 15 ga watan January na shekarar bature shine rana aihuwa na, ina kara godewa Allah da ya kyautata halitta na, ina fatan wasu shekara masu albarka a gaba, kamar yadda na baya s**ayi albarka.
Abinda muka aikata mai kyau abaya Allah ya bamu ladan sa, wanda kuma mukayi kuskure Allah ya yafe mana, hakama mutanen da na batawa abaya nasani ko bansani ba ina neman gafarar su domin ba lallai bane insane wata shekara ko shekaru a gaba.
Wudanda s**a min laifi na sani ko bansani ba na yafewa kowa, dan Allah idan kana da tunanin inada girmankai to kajiye tunaninka/ki muyi mu,amala da kai cikin amincewa juna.
Idan mun hada karaka/ki kalli na girmeka/ki ko ka/ki girmeni, girma na Allah ne.
Ina fatan zan samu haka a wurin ka/ki, Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya, Allah ya horewa kowa abinda zai ci shi da iyalansa, kowa da bukatan sa warin Ubangiji, Allahu ya biya mana.
Kuma ina rokon Allah ya raba mu da hasada da kyashi, domin sune suke mayar da mutane baya acikin al,amuran su.
Na godewa kowa da kowa da irin yadda ake kulawa da ni da iyalai na, da kuma yadda ake nuna min kauna.
Allah ya karawa rayuwarmu albarka, Amin.

✍️✍️ Auwal Ahmed Tsandon dandela ✍️✍️
👇👇
📲 08137035907🔍
📲 09129879760 🔍
Call and WhatsApp

Hello and welcome back,  we prepared a good data for at affordable price. We send you a Data every where you are, and ou...
10/01/2024

Hello and welcome back, we prepared a good data for at affordable price.
We send you a Data every where you are, and our service is very simple, just pay your money and Wait your service.
Contact me on the following numbers:
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
08137037907 👉 09129879760
Call or WhatsApp
Service account is
9437371516
Wema, Aljazirdata
8137035907
Opay, Auwal Ahmad.
👇👇👇👇👇👇 👇👇👇👇👇👇

Daga farfajiyar maulud na babban zawiyar mu dake garin BALI. Wato zawiyar Sheick Alhaji Hammawa Bali.
06/01/2024

Daga farfajiyar maulud na babban zawiyar mu dake garin BALI.
Wato zawiyar Sheick Alhaji Hammawa Bali.

TUNATARWA Yaune Insha Allahu za,a gabatar da gagarumin maulud din nan da muka Riga muka sanar abaya.Wanda za ayi a kofar...
05/01/2024

TUNATARWA
Yaune Insha Allahu za,a gabatar da gagarumin maulud din nan da muka Riga muka sanar abaya.
Wanda za ayi a kofar gidan shehinmu wato Sheick Alhaji hammawa anan cikin gari Bali.
Lokaci daga karfe 8:00pm zuwa abinda ya sawaka na wayewar gari Insha Allahu

Allah yabada ikon zuwa Amin.

HAPPY NEW YEAR IN ADVANCE The founder, Chief Executive Officer and the general manager, Alhaji Salisu Ibrahim Kantin Sau...
01/01/2024

HAPPY NEW YEAR IN ADVANCE
The founder, Chief Executive Officer and the general manager, Alhaji Salisu Ibrahim Kantin Sauki Dallatun Bakundi and Alhaji Sadam Alhaji Salisu Kantin Sauki wishing you happy new year in advance.
And we really appreciate you with the support you are giving to the Kantin Sauki Investment Company.
And also the CEO of the company Alhaji Salisu Ibrahim Kantin Sauki Dallatun Bakundi said that he has ready to bring you more products in very cheap price, and he also very proud of you by the way you are support us by buying our goods and services.
Once again say hi and happy new year 2024 in advance.
🎉🎊🎀🎁🎷🎸🎺🎻🎹🎻🥁🎤 👇👇👇

Alhamdu lillah, may thanks goes to almighty Allah who has give me the right to ma no e a wonderful visitation to Yola an...
29/12/2023

Alhamdu lillah, may thanks goes to almighty Allah who has give me the right to ma no e a wonderful visitation to Yola and Gombi in Adamawa state.
Surely a traveling is a part of knowledge, that is true.
Masha Allah, Alhamdu lillah.

`Yan kasuwa ku kara hakuri, muna kan ko karin Samar muku da hanyar tallata muku kayan ku ku ma, amma akawi sauran lokaci...
28/12/2023

`Yan kasuwa ku kara hakuri, muna kan ko karin Samar muku da hanyar tallata muku kayan ku ku ma, amma akawi sauran lokaci.
Muna kokarin yin register a affiliate marketing domin fada da tallace - tallace da mukeyi.
Amma a yanzu kam ...........😷😷😷😷😷
👇👇👇👇👇
Be patient pls. We are ready to expand our advertising program with affiliate marketing, but in few days coming, don't be an anger.

ILIMI JAGORAR DAN ADAM.Salam ina dalibai, diploma, HND  k**e yi ko degree, masu masters da yan PGD, kai harma da masu do...
20/12/2023

ILIMI JAGORAR DAN ADAM.
Salam ina dalibai, diploma, HND k**e yi ko degree, masu masters da yan PGD, kai harma da masu doctoring degree.
Ga wat a dama ta samu, muna taimakana dalibai wurin basu shawarwari akan aikin project da thesis da conference, journal dama duk abinda yayi K**a da wannan, kuma muna printing da bending, dukan wudan nan aukka namu akan farashi mai sauki.
Ku tuntube mu domin karin bayani akan wannan lines 08137035907/09129879760.
Don't hide yourself, be a wise at any moment.

Hello and good afternoon, our fellow customers, our products is available for you right now. We have different types of ...
17/12/2023

Hello and good afternoon, our fellow customers, our products is available for you right now.
We have different types of motorcycle, like Boxer, TVS, Haojue, and also we have zinc, nails and other building materials.
We have cement and blocks all at kantin Sauki investment Bali.
And we have any type of chemicals you want both for insects and grass, all these at affordable price.
Come one come all.
Just contact the managers for details our location is tiv quarters along Deeper life bible Church, in Bali town.

Address

Bali

Telephone

+2348137035907

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when In-Charge in Office posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to In-Charge in Office:

Shortcuts

Share