02/06/2026
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karɓi dan majalisar dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazabar Makoda, Hon. Muhammad Ahmad Tomas, wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar NDC zuwa APC.
Hon. Tomas, wanda a baya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NDC, ya sanar da komawarsa APC ne yayin wata ziyara da ya kai gidan Sanata Barau a Abuja ranar Litinin, tare da rakiyar shugabannin kananan hukumomin Makoda da Dambatta, Alhaji Isa Currency da Alhaji Jamilu Abubakar Dambatta.
Yayinda yake karbar Dan Majalisar, Sanata Barau ya bayyana cewa wannan sauyin wata alama ce ta yadda siyasar Kano ke sauyawa, musamman yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027