Tofa medicine store

Tofa medicine store we do sell all kind of legal drugs and surgical equipment

12/09/2026
01/11/2025

Alhamdulillah

21/08/2022

Malaria tana saka mace ta haifi yaro kafin lokocin haihuwar shi, haka kuma tana kashe yaro kafin a haife shi.

20/07/2022

Amfanin Kubewa Ajikin Dan Adam:

Mutane da dama suna amfani da kubewa a matsayin miya ba tare da sanin tarin amfanin ta ga jikin dan Adam ba.

Bincike ya nuna kubawa na dauke da sinadarai kaman haka:

Calories
Carbs
Protein
Fiber
Magnesium
Folate
Vitamin A
Vitamin C
Vitamin K
Vitamin B6

Wassu sinadaran sun hada da sinadaran kare cells da kuma lalata ta guba a jiki kaman:

- polyphenols
- flavonoids
- isoquercetin
- Lactin

Ga kadan daga cikin amfanin kubewa a jikin dan Adam:

1- Kara Karfin Gani.
Kubewa yana taimaka wajen kara karfin gani. Ko mai karatu ya san dalili, sabida yana dauke da sinadaran Vitamin A da carotene.

2- Yana taimakawa masu juna biyu:
Kubewa yana matukar taimakawa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki, domin kubewa na kunshe da dimbin sinadaran Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki da. lafiyarsa.

3- Yana rage hadarin kamuwa da ciwon koda.
Wani bincike da aka gudanar a jami’ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da cewa, yawan amfani da kubewa na matukar rage hadarin kamuwa da ciwon koda.

4- Yana taimakawa masu cutar Asthma.
Kubewa yana maganin cutar wahala wajen fitar da numfashi wato Asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita.

5- Ana amfani da kubewa wajen maganin cutar siga wacce ta zamo ruwan dare a tsakanin al'umma a yanzu. Tana dauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin dan Adam.

6- Inganta Lafiyar Uwar Hanji.
Kubewa na inganta lafiyar hanji da tumbi ta hanyar fitar da sanadaran da ka iya lahani ga hanji ko tumbin. Kuma sakamakon haka ne, ta ke maganin kumburi da cushewar ciki wanda kuma ke rage karfi ciwon siga ko ma maganinsa.

7- Kubewa Na Kara Karfin Garkuwan Jiki.
Yawan amfani da kubewa na kara bunkasa tare da karfafa garkuwar jikin dan-adam. akwai wasu Sinadarai dake cikin kubewa masu matukar amfani a garemu da s**a hada da, Bitamin C da 'Calcium' da 'Magnesium' dake taimaka wa wajen yaki da kuma fatattakar duk wata cuta da ka iya kai wa jikin mutum farmaki.

8- Yana maganin karancin jini.
Yana matukar maganin karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har ya yi wa mutum lahani ba.

9- Gyaran Fata.
Ga mai son kara inganta fatan jikin sa ya yi laushi da santsi kamar yaukin kubewar toh ya lazumci amfani da ita.

10- Rage Hadarin Kamuwa Da Ciwon Zuciya.
Kubewa na wannan aiki ne saboda wani sanadari da take kunshe da shi da ake kira 'soluble fibre' a turance, wanda ke taimakawa wajen rage 'cholesterol' wanda hakan ke rage yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya.

Lafiya uwar jiki

17/07/2022

Ka san dalilin shanyewar ƙafa bayan allura a ɗuwawu?

Shanyewar ƙafa matsala ce da ke faruwa sakamakon lahani ga jijiyar laka da ake kira da 'sciatic nerve' wace ke kai saƙonni zuwa wasu tsokokin ƙafa.

Wannan jijiyar laka ta fito daga laka ne sai ta biyo ta cikin ƙashin ƙugu sannan ta ratso ta cikin tsokokin ɗuwawu zuwa ƙafa har tafin sawu.

Wannan matsala na faruwa ne idan aka kuskure aka tsira allura a kan jijiyar lakar yayin allura a ɗuwawu, ko idan ruwan allurar ya tunzira jijiyar lakar, ko kuma idan allurar ko ruwan allurar ya kawo kumburi a kewayen jijiyar lakar wanda hakan na iya danne ko shaƙe ta har aikinta ya samu cikas.

Waɗanda suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da:

1) Wanda bai bayar da haɗin kai ba yayin yin allurar, musamman ƙananan yara da ma manyan masu tsoron allura.

2) Mai rama sosai.

3) Faɗawa hannun wanda bai ƙware ba.

4) Da kuma wanda tsautsayi ya faɗa wa.

Alamomin wannan matsala na faruwa ne a dukan rassan jijiyar lakar a ƙafa nan take ko bayan wani ɗan lokaci.

Alamomin sun haɗa da:

1. Matsanancin ciwo

2. Sagewa

3. Shanyewar tafin sawu

3) Rauni ko rashin ƙwarin ƙafa

4) Rashin ji a fata idan aka taɓa

5) Wahalar tafiya: ɗingishi, jan ƙafa da sauransu.

Da zarar an lura da waɗannan matsaloli da aka ambata a sama, a gaggauta sanar da jami'in lafiyar da ya yi allurar domin ɗaukar matakan gaggawa. Wannan matsala ana warkewa sumul kamar ba a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti na iya nakasa ƙafar.

Game da shanyewar ƙafa likitocin fisiyo (Physiotherapists) ne ke amfani da hanyoyin ƙwarewa domin yi wa jijiyar lakar da tsokokin ƙafar ƙaimi har aikinsu ya dawo yadda ya kamata.

Physiotherapy Hausa

MALARIA ----------------MALARIA: Wannan wani rashin lafiya ne da ake samunsa sanadiyyar cizon macen sauro, wadda take sa...
17/07/2022

MALARIA
----------------

MALARIA: Wannan wani rashin lafiya ne da ake samunsa sanadiyyar cizon macen sauro, wadda take sakawa mutum kwayoyin cuta a cikin jini.

A na samun cutar ne a sanadiyar kwayoyin cutar da macen sauro ke zubawa mutum acikin jini.

KWAYOYIN CUTAR DA SUKE KAWO MALARIA :

1- P falciparum
2- P Vivax
3- P ovalae
4- P malarias
5- P knowlesi

Amma amfi samun p falciparum a Nigeria shi yasa mafi yawan magani da ake amfanida shi na malaria a Nigeria ACT ne .

GA WASSU DAGA CIKIN ALAMUN MALARIA :

1- Zazzabi
2- Ciwon kai
3- Tashin Zuciya
4- Amai
5- Gudawa
6- Ciwon jiki
7- Atini
8- Dachin Baki
9- Rashin Cin Abinci
10- Rashin Karfin jiki.
11- Kasala
12- mutun yaji ya rasa abinda yake masa dadi.

GA WASSU DAGA CIKIN MUTANE IDAN MALARIA TAKAMASU RAYUWARSU TANA CIKIN HATSARI :

1- Mace Mai Ciki
2- Yara Kanana
3- Masu cutan Sickler

1- Malaria A Mace mai ciki Yakan kawo mata :

A- Haifan Macaccen jariri
B- Yakan Zubar mata da ciki.
C- Yakan Kawo Haihuwan Bakwaini .
D- Yakan Kashe Uwar Da Yaron Gabaki Daya.

YA AKE GANE MUTUM YANA DAUKE DA KWAYAR CUTAR MALARIA :

Ana gane malaria ne ta hanyoyi guda biyu wanda dukkansu jini ake gwadawa, sune :

1- RDTs Malaria test
2- Microcopy Malaria test

MATSALOLIN DA MALARIA YAKE KAWOWA ( COMPLICATION OF MALARIA )

1- Rashin jini a jiki
2- Matsalar kwakwalwa
3- matsalar Ciwon zuciya
4- Matsalar huhu da oda
5- Kumburi ko fashewar spleen .
6- Yana saukan da suga ( Hypoglycemia)

KARIYA DA KAMUWA DA CITON MALARIA :

1- SPAQ (sulfadoxine-pyrimethamine + amodiaquine) wannan wata magani ce wanda ake bawa yara kanana masu watanni 3 zuwa 59 domin kariya daga cutar malaria.

Kungiyoyin lafiya ta cikin gida da ta dubiya sun dauki nauyin bada wannan maganin kyeuta a Najeriya duba da yanayin yadda rayuwar yara kanana take shiga hatsari idan s**a kamu da Malaria.

Ana bada maganin lokocin da ruwa yafara sauka wato sakanin July da October domin itace lokocin akafi samun ciwon Malaria.

Note:

1- Yaro mai zazzabi ba'a bashi
2- Yaron da yasha septrin ba'a bashi
3- ba'a hadashi da ko wacce irin maganin malaria.

2- Fansider (sulfadoxine-pyrimethamine) ita ma wata magani ne wanda ake bawa mata masu juna domin kariya daga cutar Malaria.

Ana bada maganin ne da zarar mace cikin ta yakai watanni hudu ( 16weeks), sannan abada 2nd dose a 20 - 22 weeks sannan a bada 3rd dose a 26 weeks ( akalla ana so a samu tazarar sati 4 sakanin ko wacce dose).

3- Akoi sauran magunguna da ake amfani da shi domin kariya daga malaria kamar su:
- Proguanil
- Doxycycline
- Daraprim
- da sauran su

4- Sauran hanyoyin sun hada da:

- Shiga gidan sauro.
- Daina Barin ciyawa cikin gida .
- kiyaye tsabtan muhalli da ta bayan gida dan kada sauro su samu wurin zama.
- Kwashe shara akai akai kada abari yataru a gida.

MAGANIN ZAZZABIN CIZON SAURA :

Maganin zazzabin cizon sauro shine duk sanda akayi rashin lafiya a ziyarci asibity domin a tabbatar da shi daganan likita yabada magani .

IDAN NAJI ZAZZABI ZAN IYA SHAN COATEM ???

A,a baza kasha ba sabida shan magani barkatai yana da illa , kuma an hana shan maganin nalaria batareda an aunaka an tabbata kanada malarian ba .

Mafita shine idan kaji wayennan alamomi kaje asibity mafi kusa da kai domin ba malaria kadai bane yake kawo wadannan alamomin ba .

Lafiya uwar jiki

TAQABBALALLAH MINNA WAMINKUM
02/05/2022

TAQABBALALLAH MINNA WAMINKUM

06/02/2022

GOOD MORNING OUR CUSTOMERS.
DAFATAN KOWA YANA CIKIN KOSHIN LAFIYA

Address

Layin Abasha Damaturu
Damaturu
620252

Opening Hours

Monday 07:31 - 21:30
Tuesday 08:00 - 21:30
Wednesday 09:00 - 22:00
Thursday 08:00 - 22:00
Friday 08:00 - 22:00
Saturday 08:00 - 21:50
Sunday 08:00 - 22:00

Telephone

08021388442

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tofa medicine store posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Tofa medicine store:

Shortcuts

Share