19/07/2026
IBUPROFEN ko PARACETAMOL.
Wanne Ya Kamata Ka Fara Sha?
Mutane da yawa suna tambaya:
"Shin Ibuprofen zan fara sha ko kuwa Paracetamol?"
Amsar ta danganta da dalilin da ya sa za ka sha maganin.
Mu sauƙaƙe bayanin:
Paracetamol
Ana amfani da Paracetamol ne musamman domin:
Rage zazzabi
Sauƙaƙa ciwo mai sauƙin raɗaɗi zuwa matsakaici
Rage ciwon kai
Sauƙaƙa ciwon jiki
Yana aiki ne a cikin kwakwalwa wajen rage jin ciwo da kuma saukar da zafin jiki.
Amma yana da ƙarancin tasiri wajen rage kumburi.
Ibuprofen
Ibuprofen ma yana rage ciwo kuma yana saukar da zazzabi.
Sai dai yana da wata ƙarin fa'ida.
Shi magani ne mai rage kumburi (anti-inflammatory).
Wannan ya sa ya fi dacewa idan ciwon yana tare da kumburi, kamar:
Ciwon haƙori tare da kumburin dadashi
Murɗewar gaɓa ko rauni yayin wasanni
Ciwon amosanin gaɓoɓi (arthritis)
Ciwon al'ada ga wasu mata
To, wanne ya kamata ka fara sha? Idan matsalarka ita ce:
Zazzabi
Ciwon kai na yau da kullum
Ciwon jiki
Ciwo mai sauƙin raɗaɗi
To Paracetamol shi ne ake yawan fara ba da shawarar amfani da shi a irin wannan yanayin, domin yana da sauƙi ga ciki kuma ya dace da mutane da yawa idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata.
Amma idan ciwon yana tare da kumburi, Ibuprofen yana iya zama mafi dacewa, muddin ba ya da haɗari a gare ka idan ka yi amfani da shi.
Ana iya shan su tare?
A wasu lokuta, eh.
Likitoci na iya ba da shawarar a yi amfani da su tare a wasu yanayi, domin kowannensu yana aiki ta hanya daban da ɗayan. Amma kada a rika haɗa su kullum ba tare da shawarar Likita ko wani ƙwararren ma'aikacin lafiya ba.
Waɗanne mutane ne s**a fi kamata su yi taka-tsantsan da Ibuprofen?
Ka guji amfani da Ibuprofen ko ka nemi shawarar likita idan kana da:
Gyambon ciki (stomach ulcer)
Cutar ƙoda
Rashin ruwa mai tsanani a jiki (severe dehydration)
Rashin jituwa da magungunan NSAIDs (allergy)
Wasu cututtukan zuciya
Muhimmin Saƙo ga mai karatu:
Paracetamol shi ne mafi yawan lokuta ake fara amfani da shi wajen magance zazzabi da ciwo mai sauƙin.