First Aid Group of Jibwis Taraba State

First Aid Group of Jibwis Taraba State Wannan shafi ne na bada taimakon farko

26/08/2026

194 Riyadussaliheen Yola South

26/08/2026

Karatun AlFusul Fī Siratir
Bn Fodio, Jalingo

Mahalarta International Conference Da Suke kan Hanya Suna Bukatar Addu’oi Daga Wajen Yan Uwa Masu Albarka....
10/08/2026

Mahalarta International Conference Da Suke kan Hanya Suna Bukatar Addu’oi Daga Wajen Yan Uwa Masu Albarka....

07/08/2026

Shugaban ƙungiyar Izala, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, a madadin kungiyar da haɗin gwuiwar kungiyar Haɗa kan Musulmai ta duniya (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY, na gayyatar Al'ummar musulmi zuwa gagarumin taron ƙarawa juna ilimi mai taken 'BAMBANCE BAMBANCE TARE DA ZAMAN LAFIYAR JAMA’A”

Taron wanda 'HAƊIN GUIWA NE TSAKANIN KUNGIYAR HAƊA KAN MUSULULMAI TA DUNIYA, MAI CIBIYA A ƘASAR SAUDIYYA (RABIƊATUL ALAMIL ISLAMIY DA ƘUNGIYAR WA'AZIN MUSULUNCI TA KASAR NAJERIYA, JAMA'ATU IZALATIL BID'AH WA IKAMATIS SUNNAH.

-Za a buɗe taron conference ranar talata 11/August/2026 da misalin karfe tara na safe (9:00am) a kuma gama ranar laraba 12/August/2026 da rana 2:30pm.

-Za'a gabatar da Wa'azin kasa a harabar Masallacin JIBWIS dake helkwatar kungiyar a unguwar Utako dake birnin tarayya Abuja, daga yammacin laraba har zuwa daren alhamis.

-Safiyar alhamis 14/August/2026 kuma sai jama'a su koma garuruwansu.

Babban bako na Musamman, Shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Ahmad Bola Tunibu.

Uban Taro: Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad

Sauran manyan Baki sun haɗa da:
Gwamnoni Ministoci, Yan majalisu na tarayya da na jahohi, Iyaye Maluma, Sarakuna, yan kasuwa da sauran yan uwa musulmi dake fadin Naijeriya da sauran ƙasashen ketare.

Ana sa ran halartar manyan bakin Malamai daga manyan ƙasashen duniya insha Allah.

Sanarwa daga Sakataren JIBWIS' na ƙasa Sheikh Dr Muhammad Kabir Haruna Gombe, ta ofishin kwamitin Labaru na babban taron.

Jibwis Nigeria. . .

01/08/2026

Wa'azin Jiha wadda Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe ta Shirya Kuma take gabatarwa a garin Maidugu dake karamar Hukumar Akko.
‎
Jawabin SHEIKH Usman Isa Taliyawa Mataimakin Shugaban Kungiyar JIBWIS ta Tarayannan Nigeria
‎
‎
‎Jibwis Gombe
‎Social Media Directorate..

01/08/2026

‎Wa'azin Jiha wadda Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe ta Shirya Kuma take gabatarwa a garin Maidugu dake karamar Hukumar Akko.
‎
‎Mai Wa'azi na Biyu Seikh Imam Adam Bajoga da Alaramma Usman Umar
‎
‎Jibwis Gombe
‎Social Media Directorate.

ASSALĀMU ALAIKUM WA RAHMATULLĀHI WA BARAKĀTUHUSANARWA KAN SABBIN SAUYE-SAUYEN MUƘAMAI A MAJALISAR AGAJI TA ƘARAMAR HUKUM...
01/08/2026

ASSALĀMU ALAIKUM WA RAHMATULLĀHI WA BARAKĀTUHU

SANARWA KAN SABBIN SAUYE-SAUYEN MUƘAMAI A MAJALISAR AGAJI TA ƘARAMAR HUKUMAR JALINGO (F.A.G OF JIBWIS JALINGO DIVISION).

Shugaban Majalisar Agaji ta Ƙaramar Hukumar Jalingo (F.A.G of JIBWIS Jalingo Division), ƙarƙashin jagorancin Mallam Bashir Isa, ya amince da sauye-sauyen muƙamai a majalisar kamar haka:

Usama Muhammad Bello – Sakataren Majalisar Agaji ta Ƙaramar Hukumar Jalingo.

Mallam Auwalu Abdullahi Adamu – Mataimakin Sakataren Majalisar Agaji ta Ƙaramar Hukumar Jalingo na II.

Nasiru Ibrahim – Mataimakin Sakataren Shirye-shirye na Majalisar Agaji ta Ƙaramar Hukumar Jalingo na III.

Abdullahi Ibrahim Banyam – Mataimakin Mai Ladabtarwa na Majalisar Agaji ta Ƙaramar Hukumar Jalingo na I.

Idris Zakari – Auditor I.

Aliyu Muhammad – Auditor II.

Shamsuddin Adam – Assistant Intelligence Officer.

Umar Adam Nta – Assistant Group Leader.

Musa Saeed – Assistant Operation Officer.

Usman Adam Nta – Division Circular Bearer.

Rabi'atu Ibrahim Qala – Assistant Circular Bearer.

Shu'aibu Abubakar Yayaji (Master) – Division Quarter Master.

Mu'azu Jikan Shehu (Murde Murde) – Assistant Patron.

Muna taya dukkan waɗanda aka ba waɗannan muƙamai murna, tare da yi musu addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba su ikon sauke nauyin da aka ɗora musu cikin gaskiya, riƙon amana, adalci da tsoron Allah.

Allah Ya sanya wannan alheri ya zama sanadin ci gaban Majalisar Agaji da kuma JIBWIS baki ɗaya. Āmīn.

Sanarwa daga:
Usama Muhammad Bello
Sakataren Majalisar Agaji ta Ƙaramar Hukumar Jalingo
F.A.G of JIBWIS Jalingo Division
18 Safar 1448AH
1 August 2026M

Allah Ya ba mu da sauran jami'an da aka naɗa ikon gudanar da wannan amanar cikin nasara da albarka.

30/07/2026

Live streaming of Abubakar Albashir Dangata

27/07/2026

11 Kashfush Shubuhāt
@ Bn Bāz, Jalingo

16/07/2026

Live stream

Karatun Littafin:
Adabul Mufrad

Darasi na 29

Tare da Sheikh Abubakar Imam Abbas Fullatee
Daga Masjid Bin Fodio

Ayi Sauraro Lafiya
01/02/1448= 16/7/2026

Address

Jalingo

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when First Aid Group of Jibwis Taraba State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share