AURE KO SAKII

AURE KO SAKII MASHA ALLAH
MASHA
ALLAHUAKBAR

04/06/2026

Daga lokacin da ka soma dukan matar ka
kasani kana mata training ne na busar mata da zuciya.
Matar ka ba jaka bace.

KADA KI ZAMA UWA KAWAI...Ki kula da tsabtar tunanin ɗanki daga munanan kalmomi da maganganu marasa kyau, kamar yadda k**...
04/06/2026

KADA KI ZAMA UWA KAWAI...

Ki kula da tsabtar tunanin ɗanki daga munanan kalmomi da maganganu marasa kyau, kamar yadda k**e kula da tsabtar tufafinsa a kowace rana.

Ki ciyar da hankalinsa da ingantacciyar aƙida kamar yadda k**e ciyar da jikinsa da abinci.

Ki kula ya riƙa yin sallolinsa a kan lokaci, kamar yadda k**e kula da jadawalin cin abincinsa.

Ki kula da zuwa Masallaci da kuma haddar Alƙur’ani, kamar yadda k**e kula da zuwa Makarantarsa.

Maimakon ki riƙa ba shi labaran ƙarya da tatsuniyoyi kowane dare, ki riƙa ba shi labaran Annabawa, Sahabbai, Tabi’ai, da salihai, domin ya ƙaunace su kuma ya yi koyi da su.

Ki koya masa ma’anar “La ilaha illallah” kafin ki koya masa haruffan baƙaƙe.

Ki riƙa gaya masa labarin Aljannah kafin ki riƙa gaya masa labarin duniya.

Ki sa ya so Lahira tun yana ƙarami, kafin ya girma ya fara jin tsoronta.

Ki koya masa girmama manya, da ladubban cin abinci, da kuma sada zumunci.

Ki koya masa kyawawan halaye da ɗabi’u.

Ki zama uwa mai girma, ki yi niyyar tarbiyyarsu domin Allah, domin Allah Ya sanya albarka a cikinsu.

Ki tashe su cikin ingantacciyar tarbiyya, har idan sun shiga shagulgulan rayuwa, su riƙa ɗaukar masallaci a matsayin hanya, abokai na gari a matsayin mafaka, Alƙur’ani a matsayin aboki, Aljannah kuma a matsayin buri.

Ki zama uwa abin koyi a tarbiyya.

Ki zama abokiya, masoyiya, kuma kusa da su, ba uwa kawai ba.

Al’umma tana buƙatar mazaje masu ƙarfi, waɗanda ba sa jin tsoron zargin kowa a cikin abin da ya shafi Allah, kuma duniya ba ta shagaltar da su daga Lahira.

Saboda haka, ki zama ke ce wadda za ta gina su.

Allah Yasa mu amfana.

27/05/2026

Yauce fa Sallah
Honorable zan iya aski ko nakara jira🙄??

Mutanen da s**a yi shahada kenan a ranar arafah Allah ya amshi shahadar su🤲
27/05/2026

Mutanen da s**a yi shahada kenan a ranar arafah
Allah ya amshi shahadar su🤲

*😭 KA SAN ME YAFI BAN TSORO A RANAR ARFAH ? 😭**Ba talauci bane… ba rashin lafiya bane… ba matsalar duniya bane…*Abin tso...
26/05/2026

*😭 KA SAN ME YAFI BAN TSORO A RANAR ARFAH ? 😭*

*Ba talauci bane… ba rashin lafiya bane… ba matsalar duniya bane…*

Abin tsoro shine: Ranar Arfah ta zo… ta wuce… Allah bai gafarta maka ba. 💔

Ya kai bawan Allah…

Akwai dare da mutane suke kuka a cikin kabari yanzu. Ba saboda zafi kawai ba… a’a…

*Suna kuka ne saboda: sun samu damar yin addu’a amma s**a yi wasa da ita. 😭*

Wata mata yanzu tana ƙarƙashin ƙasa… shekarar da ta gabata tana cewa:

> “Ai idan Arfah ta zo zan gyara rayuwata…”

*Amma bata kai Arfah ta bana ba. 😭*

Wani saurayi kuma yace:

> “Har yanzu ni matashi ne…”😭

*Yau tsutsotsi suna cin jikinsa. 💔*

Kai kuma har yanzu kana numfashi…

Ka sani kuwa ? Wataƙila Allah ya raya ka zuwa Arfah ne domin ya ji kukanka… ba saboda ka cancanta ba. 😭

💔 Kada ka bari ranar ta same ka cikin:

sakaci, kallon haram, yawan dariya, ko nuna wa mutane ibada.

📿 A ranar Arfah… akwai bayin da:

zasu ɗaga hannu da hawaye, zasu tuna da zunubansu, zukatansu zasu karye saboda tsoron Allah…

Sai Allah yace wa mala’iku:

> “Ku shaida… Na gafarta musu.” 😭

😭 Amma akwai wasu kuma… rana zata zo ta tafi:

babu tuba,

babu nadama,

babu kuka,

babu komawa ga Allah.

Su ne mafi asara. 💔

Ya kai bawan Allah…

Ka taɓa yin addu’a da zuciya ta girgiza ? Ka taɓa kuka saboda tsoron haduwa da Allah ? Ka taɓa cewa:

> “Ya Allah… idan ka barni da zunubaina… ni na halaka…” 😭

*✨ Wallahi…* Akwai addu’ar da idan ta fito daga zuciya mai gaskiya:

zata canza rayuwarka,

zata bude maka ƙofofin alheri,

zata zama sanadin tsira ranar Alqiyama.

🤲🏻 Saboda haka idan Arfah ta zo: Ka manta da mutane. Ka manta da wayarka. Ka shiga sirri tsakaninka da Allah.

Sannan ka ce:

> “Ya Allah… na zo maka da zuciya mai rauni… da zunubai masu yawa… amma na san rahamarka ta fi girma…” 😭

> “Ya Allah… idan ka gafarta min… babu wanda zai cutar da ni… idan ka barni… babu wanda zai taimake ni…” 😭

😭 Kada ka bari wannan rana ta wuce kamar sauran kwanaki…

Allah ya yafe mana.

24/05/2026

‎Ya Allah
Ka cire mana damuwar da take zuciyarmu
Ka maye mana gurbin ta da hasken imani.

24/05/2026
22/05/2026

Zaka iya siyar da wayarka📱
wadda kake chatting ka yiwa budurwarka dinkin sallah😎?

Address

Zaria
Kaduna
AURE

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AURE KO SAKII posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share