Health talk free.

Health talk free. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Health talk free., Medical and health, Kofar Fada Kankara, Katsina.

11/05/2026

Duk Wadannan Magungunan na supplements aikin Banza ne, daga Karshe Kasuwa Suke da anshe Maku Kudi Babu biyan Bukata sai illa gaba.

10/05/2026

Wani lokaci mutum zaiji zafin kirji, zafin zuciya da haki ya dauka hawan jini ne ko ulcer, karshe awo ne zai tabbatar.

30/04/2026

ALAMOMIN FARKO FARKO NA ALAMUN CIWON ZUCIYA GA MUTUM.

1- Karancin Nunfashi
2- Yawan Gajiya
3- Kasa aikin Kome Koda tafiya ce
4- Ciwon kafafu
5- Yawan Zuwa Fitsari
6- Kunburin Kafafu da Ciki

Duk Wanda ya Fara ganin wadannan alamomin a tare dashi ya daina wahalar tunanin Ulcer, a binciki yanayin aikin Zuciya.

26/04/2026

WADANNE ABABE KO MATSALOLI SUKAFI HAIFAR DA YAWAN ZUBEWAR CIKI?

Barkan mu da Yamma

Kamar yanda nasha rubuce rubuce akan matsala ta zubewar ciki ababen basa karewa. Yawan zubewar ciki matsala ce dake haifar da damuwa ga iyalai musamman a bangaren uwar gida ita da take shan wahala da ukuba ta ciki daga karshe kuma cikin ya zube Allah sarki!

NA FITO DA WASU DALILAI NA KUSA KUSA DAKE HAIFAR DA HAKAN GA MATA.

Zaka samu mata suna daukan ciki amma daga baya ya zube to meya sa ake samun hakan? To ga kadan daga ciki sai ayi taka tsantsan da bincike ko nazari dan kaucewa hakan gaba.

- Anfani da magungunan ACNE Ga mata, idan mace na yawan anfani da maganin kurajen fuska sukan sa yawan zubewar ciki.

- Infections

- Matsala ta mahaifa

- Rashin nagarta ta al'aurar mace

- Matsala ta sugar

- Muhalli, sana'a ko dabi'u

- Yawan shaye shayen magunguna

- Shan taba da giya ga mata

- Matsala ta hormonal changes

- Rashin nagartar kwan halitta na mace.

Idan iyalai nada wannan matsala sai a duba.

Ana anfani da magunguna ko shawar warin likita daidai da abunda aka tabbatar da itace matsalar daga cikin wadannan matsalolin dana zayyana.

25/04/2026

CIN ABINCI A LEDA KO TAKEAWAY.

Illar cin abinci a cikin leda baƙa kokuma (takeaway na soso) na da illa da dama ga lafiya, musamman idan an zuba abinci mai zafi ko me maiƙo a cikinta.

ILLOLIN DA YAKE HAIFARWA

1. Ciwon daji (Cancer): Lokacin da leda ta hadu da zafi sosai, tana fitar da wasu sinadarai masu guba (kamar BPA da phthalates) da ke iya shiga abinci. Waɗannan na iya ƙara haɗarin cutar daji idan ana yawan amfani da su.

2. Cututtukan ciki: Abincin da ya haɗu da sinadarai daga leda na iya haddasa tashin zuciya, gudawa, ko matsaloli a hanji.

3. Illa ga hanta da Ƙoda: Wasu sinadarai daga leda na iya taruwa a cikin jiki, suna jawo illa ga hanta da ƙoda.

4. Illar jiki da ciki (Pregnancy): Ga mata masu juna biyu, yawan cin abinci daga leda na iya shafar cigaban jariri tare da kawo naƙasu (tawaya ko deformity) ga jaririn da zasu haifa

Saboda haka, yana da kyau a guji zuba abinci mai zafi ko me maiƙo a cikin leda.

A dinga amfani da kwanon karfe, roba mara guba (BPA-free), ko tangaran ko wasu nau'o'in kayan cin abinci wanda aka amince dasu.

Riga-kafi yafi magani

03/04/2026

Amfanin shan ruwa a zaune ga lafiyar dan adam baya da kasan cewar Shan ruwa a zaune Sunnah ne.

03/04/2026

Tabbas Daukan Wani Ciki Baya sa a Zubar da Cikin da aka Samu, Allah Baya dora ma Rai Wani abu wanda yasan ba zata iya ba.

03/04/2026

Numbers of newly tested HIV positive patients in Nigeria (Jan-Mar, 2026)

1. Lagos: 2,298
2. ⁠Benue: 1,949
3. ⁠Akwa Ibom: 1,159
4. ⁠Rivers: 1,137
5. ⁠Anambra: 1,013
6. ⁠Kaduna: 842
7. ⁠Delta: 803
8. ⁠Oyo: 763
9. ⁠Ogun: 751
10. ⁠Plateau: 662
11. ⁠Imo: 640
12. ⁠Nasarawa: 615
13. ⁠Taraba: 605
14. ⁠FCT: 579
15. ⁠Abia: 527
16. ⁠Edo: 512
17. ⁠Enugu: 479
18. ⁠Kano: 476
19. ⁠Kogi: 422
20. ⁠Cross River: 396
21. ⁠Niger: 387
22. ⁠Adamawa: 382
23. ⁠Ondo: 379
24. ⁠Kwara: 329
25. ⁠Osun: 279
26. ⁠Bayelsa: 264
27. ⁠Ebonyi: 253
28. ⁠Gombe: 252
29. ⁠Borno: 238
30. ⁠Katsina: 216
31. ⁠Bauchi: 210
32. ⁠Kebbi: 196
33. ⁠Jigawa: 177
34. ⁠Zamfara: 140
35. ⁠Ekiti: 129
36. ⁠Sokoto: 110
37. ⁠Yobe: 100

Only Benue, Kaduna and Plateau made it to top from the North, and we all know why.

29/03/2026

Matan Da ke da juna biyu su sani magungunan kurajen Fuska ka iya zubar masu da ciki Basu sani ba.

Address

Kofar Fada Kankara
Katsina
234

Telephone

+2348066537033

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Health talk free. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Health talk free.:

Share