ISMA Medical Care Initiative

ISMA Medical Care Initiative Wellness

26/04/2026
28/03/2026

WASU TAMBAYOYI DA SUKE TA YI MIN YAWO A ZUCIYA A KAN KOKEN SHAIK ABDULJABBAR KABARA DAYA BAYYANA : AN SO AYI AMFANI DASHI DAGA KASAR IRAN DOMIN AYYUKAN CIN AMANAR ƘASA DA KUMA ƘIN AMINCEWARSA NA DA ALAƘA DA HALIN DA YAKE CIKI YANZU !!!

Da farko dai har yanzu muna kan matsayarmu ta kasancewar Shaik Abduljabbar Kabara mazlumi kuma bamu gushe ba muna addu'ar Allah ya gaggauta kawo masa mafita da yayewa , tare da goyon bayansa cikin neman ƴancinsa .
Sai dai tun jiya da naga wasu takardu masu shafi 13 da yaren Hausa da aka saki a shafin hukumar makarantar Malamin da yake bayyanawa babban alƙali kokensa akan shari'arsa har ya bayyanawa wani sirri da ya daɗe yana ɓoyewa (a da'awar sa) ta ƙoƙarin sa shi yaci aamanar ƙasa da kwangilar maida shi k**ar Khumainin Najeriya da kuɗaɗe masu nauyi daga kasar Iran amma yaƙi amincewa wanda yake zargin hakan na da alaka da ci gaba da zamuntarsa , sai wasu tambayoyi suke ta min yawo daga cikinsu :

1 . Me yasa wannan maganar bata tashi ba sai a yanzu a yanayin da kasar Iran take ciki ?!

2 . Shin dama ƙasar Iran tana zuwa ta kirkiro wasu jama'a ko wani mutum a wata ƙasa da sunan suyi mata aikin kafa irin gwamnatin Musuluncin da ta kafa a 1979 ?

3 . Idan tana yi mai yasa bata yi amfani da irin su Shaik Ibrahim Al-Zakzakiy da shi yana da wannan fikrar ta samuwar gwamnatin Musulunci tun kafin ma ya haɗu da Iran ko a yi juyin juya halin 1979 a Iran ?

4 . Me yasa ba a nemo wani daga cikin ƴan Shi'a a Najeriya da Iran ta raina a fannin ilmi da tunani ba sai shi Malamin ?
Wai shin da gaske malamin ne ya fitar da wannan takardun kuwa ?!

5 . In kuma daga Ahlus Sunnah Iran take so me yasa sai Shaik Abduljabbar Kabara?
Akwai wandanda s**a fishi tasiri da yawqn mabiya daga wanda ba Shi'a ba a Najeriya ne yasa shi shi ɗin ?

6 . In ma tunanin ne na kafa gwamnati akwai irin ƴan Tajdidi da masu irin fahimtar me yasa ba ta jawo su a jiki ba ?

In aikin cin amanar ƙasa ne akwai wanda s**a dace suyishi k**ar ƙungiyoyin tawaye ko masu wannan tunanin na kifar da gwamnati ke yasa Iran bata nemesu ba ?

7 . Idan kwangilar ta tabbata ta faru me yasa bata biyo ta hanyar wasu da aka sani da tunanin kafa tsarin Musulunci a Najeriya ba sai ta hanyar tsohon ministan ilmi (Malam Adamu Adamu) da ko a yan Shi'ar Najeriya ba a sa shi a ɓangaren masu ra'ayin juyin juya hali a Najeriya ?

8 . A wani karatu na Malam Abduljabbar yana raddi ga masu tuhumarsa da yiwa Iran aikin yaɗa Shi'a yayi musu raddi da cewa : Shi Iran din ma tazo ta dafa masa da kudin sai me kuma ya nuna duk wata ɗawainiyarsa da yake Iran da aljihunsa yayi ko kudin internet ma shi ya biya ....ko wata magana mai k**a da haka ..
Shin malamin ba ya tunanin wannan dafawar Iran tazo yi masa ta wannan salo ba batun juyin juya halin kafa gwamnati ake so ayi ko cin amanar ƙasa ?

9 . Shin aikin da Ayatullahi Khumaini (R) yayi a Iran cin amanar ƙasa ne ko kuma yinsa a Najeriya ne cin amanar ƙasa da ta'addanci ?

10 . Malamin ya bada labarin yanda ta kaya da su da ambasadan Iran da Malam Adamu Tsoho...ko dai labaran da Malam Adamu Tsoho ya bashi labari ne na ƙoƙarin sanar da shi abinda ya faru a Iran tunda hira ta kawo an ambaci Ayatullahi Khumaini?

11 . A labarin da muka sani Malam Adamu Tsoho har ya koma ga Allah ba shi da ko gidan kansa to amma ta yaya yake yiwa kasar Iran wannan kwangila ta ɗaruruwan miloyoyi amma ya rayu cikin wannan hali?

12 . Anya babu lauje cikin naɗi a wannan lamari da wani ɓangare na uku yake shiryawa ba tare da Malam Abduljabbar ya sani ba ko kuma su mutanen da ya ambata sun sani ko kuma ana so a haɗa ƴan Shi'a da ɓangaren na shi rikici don a kawo raunin kyakkyawan fata da ya bayyana cikin al'umar da alaƙarsu?

13 .. Ko dai rashin fahimtar wasu abubuwa ta shiga wasu gaɓoɓi na labarin nan ?
Domin bana tunanin Malamin yana da wani abu na ƙulli akan Iran ko su mutanen da abin ya faru tare da su , to mene ne ya faru ?

14 . Ina batun rawar da manyan magautan malamin na tali-tali s**a taka a abinda ya faru da shi tun farko kuma wace fuska ce za ta haɗa lamaran biyu ?

15 . Me yasa abun bai zama yana da alaƙa da ƙasar Saudiyyar da ya bayyana yana tsoron shigar ta shaida yanda yayiwa da'awar mabiyansa dukan mutuwa a Najeriya ?

16 . Batun kuɗi da ya maimaitu tsakanin malamin da wasu ƴan Shi'a a Najeriya kuwa , ko dai irin kuɗin nan ne da ƙungiyoyi ko cibiyoyin Shi'a na ƙoƙarin kusanto da juna tsakanin mazhabobi suke kashewa wajen gayyatar su taruka , raba littattafai , taimakawa da sauran su ?

An ya abun ba yana da alaƙa da irin waɗannan ƙungiyoyi ne ba wai da ƙasar Iran kai tsaye ba ?

17 . Shin dama akwai hanyoyin da ƴan Shi'ar Najeriya za su iya bi su samar da irin waɗannan maƙudan kuɗaɗen amma s**a zauna a yanayin da suke kuma basa yiwa muballigansu irin wannan tayin ko gata sai wanda ba ɗan Shi'a ba ?
Me yasa suke ƙoƙarin ƙosar da na waje ga na gida yana jin yunwa ?

18 . Ƙasar Iran ko irin waɗancan ƙungiyoyin suna gayyatar malamai da ba shiga ba da mawaƙa ciki har an gayyaci yayan Malamin ya k**ata s**a su fito suyi bayanin me s**a gani kuma me aka ce musu da s**a je , ko dai suma an musu tayin ne ?

Za mu so duk wanda sunansa ya fito a wannan wasiƙa ta shi ya fito yayi bayani don duniya ta fahimci gaskiyar al'amari da daidaito domin magana ce mai haɗari.
Daga sanda suk fito s**a yi bayani sai kuma muzo muyi tsokaci akai , domin muma za mu iya cewa wani abu akan lamarin muma a sa'ar nan , duk da dai ba a so raina nayi magana ba kuma bana fata na kara yi , sai dai kuma kashi ! Abun zai bawa wasu maƙiya ƙofa akan Shi'a da Shi'anci!

Kuma ba ina son nace abinda malamin ya fada ƙarya ne , a'a sam , sai dai tambayoyi ne da s**a yi ta min yawo a rai , kuma Ni a iya kyakkyawan zaton da nake an samu tashin fahimtar wasu lamura ne ko wata matsala daban ta faru .....kuma ba muna kare wani ɓangare bane sam .

Wallahul musta'an !!!

✍️ Khãdimul Ashrãf Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

7 / Shawwal / 1447H - 27 / 3 / 2026 Miladiyya.

https://t.me/tafarkintsiratv

Gobe Asabar Za'a Fara SHAYI a Katsina,Sashen Lafiya Na Harkar Musulunchi (ISMA) Daliban Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na fa...
13/12/2024

Gobe Asabar Za'a Fara SHAYI a Katsina,

Sashen Lafiya Na Harkar Musulunchi (ISMA) Daliban Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na farin cikin sanar da al'umma shirin fara gudanar da SHAYI / KACIYA k**ar yanda aka saba gabatar wa a kowace shekara a gobe Asabar - Lahadi 12th -13th Jimadal Thany, 1446 (14th - 15th December, 2024) insha Allah!

Ana bukatar a kawo yaran👬da za'a yiwa KACIYAR da karfe 6 na safe. Za'a fara Screening da tantance yaran @6:30am,

Za'a dauki sunayen yara (30) a kullum a tsarin wanda ya fara halartar muhallin gabatar da KACIYAR @ Markaz Katsina

Akwai tsarin DRESSING 🧻a ranakun Litinin da Talata ga yaran da aka yiwa KACIYA , insha Allah,

Iyayen yaran da za'a yiwa KACIYA su bincika su nemi ADDU'AR🤲🏻 da ake karantawa yara a 📚 Addu'o'i Ma'asurai daga A'immah🕋(SA) kafin da bayan gabatar da SHAYI domin samun tsari daga dukkan sharri da karin albarka ga 'ya'yan mu,

Ana iya tuntubar wadannan Numbers domin karin bayani:

+234 706 326 8186
+234 803 654 3231

✍🏼 ismakatsinamedia

Address

Zaria
Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ISMA Medical Care Initiative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to ISMA Medical Care Initiative:

Share