27/03/2025
ZUBAR JINI GUDAJI-GUDAJI KO KUMA WANI ABU MAI K**A DA TSOKAR NAMA A LOKACIN JININ AL’ADA (MENSTRUAL CLOT)
Jinin al’ada yana fita ne daga al’aurar mace wacce ta balaga, a duk bayan wasu kidayayyun kwanaki. Fitar jinin yana nufin mace ta kai munzalin da zata iya daukar juna biyu matukar namiji ya sadu da ita a lokacin da ya dace. Abinda yake kawo fitar jinin shine, jikin bangon mahaifar mace yana kumbura kuma ya cika da jijiyoyin jini. Wannan shiri ne na musamman domin karbar kyankyasasshen kwai na haihuwa (fertilized o**m) bayan saduwar aure. Kumburin da mahaifa take yi yana matsayin wata shimfida ce mai laushi domin samar wa kyankyasasshen kwan makwanci mai kyau da kuma abinci. Idan ba’a dace da samun kyankyasasshen kwai ya shiga cikin mahaifar ba, to, shimfidar zata zagwanye ta lalace, sai ta fita daga cikin mahaifa a matsayin jinin al’ada. Wannan abin zai rika faruwa lokaci bayan lokaci gwargwadon yadda Allah ya tsara halittar jikin mace. Ma’ana wasu matan ala’darsu takan zagayo duk bayan kowane kwana 14, ko 20, ko 30 da makamantan haka, wanda likitoci suke kira “menstrual cycle”. Wasu matan kuma basu ganin zuban jini, sai dai suga digon jini kwai wanda ake kira “spotting”.
Sa’annan mafiyawan mata suna ganin wasu alamomi idan al’adarsu ta kusa zuwa (premenstrual syndrome), wadanda s**a hada da:
1. Ciwon mara mai tsanani ko maras tsanani
2. Ciwon baya ko kugu
3. Ciccikowar nono ko ciwon nono
4. Bacin rai da rashin walwala
5. Zafin jiki ba tare da zazzabi ba
6. Tashin zuciya ko yin amai
7. Ciwon kai ko yawan mutuwar jiki
YANAYIN JININ AL’ADA
Launin jinin al’ada yakan bambanta tsakanin mata. Mafi yawanci yakan kasance jazur (red), amma wasu s**an ganshi baki-baki (dark). Idan kuma ya kusa daukewa sai ya koma kamar ruwan nama (brown). Jinin al’ada mai launi jazur yana nuna cewa bai dade sosai a cikin mahaifa ba. Mai launin baki-baki kuma yana nuna cewa ya dade a cikin mahaifa. Amma idan ya kasance ruwan kwai (orange), ko ruwan toka (grey),