24/07/2026
YADDA AKE YIN SALLAR JANA'IZA❤️🩹.
Da Farko yana da kyau musan wasu hukunce-hukunce Game da sallar Jana'iza.
—Sallar Jana'iza ba ta da ruku'u, sannan ba ta da sujada kuma bata da Tashahhud kuma ita Ana yin ta ne a tsaye.
— Idan mamacin namiji ne, liman yana tsayawa kusa da kansa.
— Idan mace ce, liman yana tsayawa kusa d tsakiyar jikinta.
Bayan anyi Alwala abinda ake fara yi shine.
NIYYAH
A yi niyyar yin Sallar Jana'iza saboda Allah.
Mu sani cewa ita niyya ba a furta da baki, domin babu hujja daga Annabi Sallallahu alaihi wasallam ko Sahabbai akan haka ( a zuciya akeyin ta)
BAYAN NIYYA TANA DA KABBARA GUDA HUƊU.
A KABBARA TA FARKO1️⃣
Bayan anyi KABBARA sai a karanta Suratul Fātiha.
(Sahih al-Bukhari, Hadisi na 1335)
KABBARA TA BIYU2️⃣
bayan an sake wata KABBARA sai ayiwa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama salati irin wanda akeyi a tahiyyah.
(Sunan Abi Dawud, Hadisi na 3199 – Albani ya inganta shi.)
KABBARA Ta UKU3️⃣
Bayan anyi KABBARA TA uku sai ayi ma mamaci addu'a.
Daga cikin addu'o'in da s**a tabbata akwai:
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدِ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَمَا نَقَّيْتَ الثَّوْبَ الْأَبْيَضَ مِنَ الدَّنَسِ...
(Sahih Muslim, Hadisi na 963)
Idan mace ce, a canza lafazin له zuwa لها.
KABBARA TA HUƊU 4️⃣
Bayan Anyi KABBARA Ta huɗu sai a yi ɗan addu'a idan ana so.
Daga cikin addu'o'in da malamai s**a ambata akwai:
اللهم لا تحرمنا أجره، ولا تفتنا بعده، واغفر لنا وله.
Ma'ana: Ya Allah! Kada Ka hana mu ladansa, kada Ka fitine mu bayansa, kuma Ka gafarta mana da shi.
SAI AYI SALLAMA.
Babu wata addu'a tak**aimai da ta tabbata daga Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam ) bayan KABBARA ta huɗu. Saboda haka, idan mutum ya yi sallama kai tsaye bayan KABBARA tahuɗu, batare da ma yace komai ba to sallarsa ta inganta in sha Allahu.
Mafi ingancin yadda zakayi sallamar shine.
السلام عليكم ورحمة الله