04/12/2023
A kiyeye yawan Shan Zaki, musamman "kafi-sukari"
Bambanci Tsakanin Tataccen Sukari (Refined Sugar) da Wanda Ba Tatacce Ba (Chemical Sugar)
A yayin da sukari (sugar) yayi tsada, wasu mutane sun koma amfani da Kafi-Sukari (Artificial Sweeteners), musamman masu shayi da masu yin wasu nau'in kayan zaƙi.
Amma Mutane da yawa basu san bambancin waÉ—an nan nau'in sukarin ba.
Tataccen Sukari (Refined Sugar) shi ne wanda ake samun shi daga irin su RAKE sannan kuma ana sarrafa shi domin tace shi da tsaftace, yana É—auke da sinadarin SUCROSE. Kun ga shi asalin shi na halitta ne (Natural). Misalin shi, irin sukari na su Dangote, Bua, Sukari Mai Dunkule (Cube Sugar)
Shi kuma Kafi-Sukari (Chemical Sugar) sukari ne da ake samar da shi a dalilin sarrafa wasu Sinadarai (Chemicals) har su bayar da zaƙin da ake so (Artificial Sweeteners). Misali: "Saccharin/Kafi-Sukari", "Aspartame" da sauransu.
Abin Lura shi ne, dukkan nau'in Sukarin in aka fiye amfani da su ba bisa ka'ida ba suna da barazana ga lafiyar mutum. Amma fa su wannan "Chemical Sugars/Artificial Sweeteners" sun fi illa.
Hasali ma akwai bincike da ke alaƙanta amfani da wasu nau'in "chemical sugar" da yiwuwar kamuwa da ciwon daji (cancer), duk da cewa kamfanonin da suke yin su, sun ce binciken baiyi adalci ba. Toh dai su kasuwanci suke yi.
Babu amfanin yawan shan sukari, ko samɓada shi da yawa a kunu/koko, shayi, zobo, da duk wani nau'in abin sha.
Wanda basu da aure, ku tabbata masu shayin da kuke zuwa wajen su shan shayi Sukarin arziki suke amfani da shi ba KAFI-SUKARI ba.
Allah ya ƙara ma ingantaccen lafiya, naku a koda yaushe, Pharm. Musa A Bello ɗan Zaria