24/06/2026
Part 2: 🤔 Me zai faru idan na ce wasu daga cikin abubuwan da muke yi domin nuna ƙauna ga yaran mu ne ke sa TV da wayar salula s**a fara karɓar aikin tarbiyya daga hannun mu?
A Part 1 mun fahimci cewa ba a haihuwar yaro da son waya ko TV, a hankali yake koyon hakan.
Amma yanzu tambayar ita ce:
🤔 Me yake sa wasu yara su kasa rabuwa da waya, yayin da wasu kuma suke iya amfani da ita yadda ya dace?
Sau da yawa, amsar tana cikin wasu kura-kurai guda bakwai da muke yi a gida ba tare da mun sani ba. Ku biyo domin sanin wadannan kura-kuran.
1. Yin Amfani Da Waya Domin Dakatar Da Kuka Ko Hayaniyar Yaro. Wannan yana daga cikin kura-kuran da aka fi yawan yi.
* Yaro ya fara kuka, Sai a ba shi waya.
* Yaro ya fara hayaniya, Sai a kunna masa cartoon.
A wannan lokacin muna tunanin mun warware matsalar. Amma a zahiri muna koya wa ƙwaƙwalwar yaron cewa:
"Idan kana cikin damuwa ko rashin natsuwa, mafitar ka ita ce waya."
A hankali yaro yana fara dogaro da waya domin samun farin ciki ko natsuwa maimakon koyon yadda zai sarrafa yanayin zuciyar sa idan yana cikin damuwa.
2. Rashin Sanya Dokoki Da Iyaka Tun Da Wuri Akan Amfani da Waya
A wasu gidaje babu lokacin TV, Babu lokacin waya, Babu sanya iyaka akan abin da za a kalla.
Kullum lokacin kallon ne da zarar akwai wutar nepa ko kuma ba'a lura da me ake kallo.
Gaskiyar magana ita ce:
Yaro ba zai iya koyon sarrafa kansa ba idan babu wanda yake koya masa inda iyaka take.
Iyaye ne ke da alhakin tsara iyakokin da za su taimaka masa ya yi amfani da fasaha cikin hikima.
3. Iyaye Ma Waya ta tafi da Tunanin su
Yaro yana koyon abu ne ta gani kafin magana.
Idan kullum yaro ya ga:
* Uba yana kan waya.
* Uwa tana kan waya.
* Kowa yana kallon waya.
To saƙon da zuciyar sa ke karɓa shi ne:
"Waya ita ce abu mafi muhimmanci a rayuwa."
Ba za mu iya koyar da abin da ba mu aikata ba. Yara suna kallon rayuwar mu fiye da yadda suke sauraron maganganun mu.
4. Barin Intanet Ta Koya Masa Abin Da Ba Mu Sani Ba. A da iyaye ne ke zaɓar abin da yara za su kalla.
Yau kuma a wasu lokuta algorithm ne yake zaɓa musu.
Misali a YouTube ko Facebook idan yaro ya shiga bidiyo na ɗaya, to ko wane video zai iya biyo wa na biyu (ko na kwarai ko na banza).
A hankali yana kallon abubuwan da iyayen sa ba su ma san suna wanzuwa ba.
Tambayar ita ce:
🤔 Idan ba mu san abin da yake kallo ba, ta yaya za mu san irin tunanin da ake gina masa?
5. Rashin Zama Da Yara
Wannan wani sirri ne da iyaye da yawa ba sa lura da shi.
Wasu lokuta matsalar ba waya ba ce. Matsalar ita ce babu wanda yake da lokaci domin yaro.
Yaro yana buƙatar:
A saurare shi, a yi hira da shi, a yi wasa da shi, a ji abin da yake damun sa.
Idan bai samu wannan kusanci daga iyaye ba, zai fara neman abin da zai cike wannan gurbi.
Sau da yawa kuma TV ko waya ce ke shiga wannan wurin.
6. Rashin Samar Da Madadin Waya
Wani lokaci muna son rage amfani da waya.
Amma babu wani abu da muka maye gurbinta da shi.
Babu karatu, Babu wasanni, Babu ayyukan gida, Babu wata sana'a ko wani abu da zai shagaltar da yaro.
Idan aka cire waya ba tare da madadi ba, zaiyi wahala a samu abinda ake so.
Domin an cire abin da yake sa shi nishaɗi, amma ba a ba shi wani madadin ba.
7. Barin Waya Ta Maye Gurbin Zama Da Iyali
Wannan yana daga cikin manyan kura-kuran da ba a cika lura da su ba.
A wasu gidaje: Uba yana kan waya, Uwa tana kan waya da saura yara, kowa yana kan waya.
Kowa yana gida amma babu wanda yake tare da wani saboda hankalin ya koma kan waya.
A hankali hira tana raguwa, Fahimtar juna tana raguwa da kuma dangantaka tana raguwa.
Alhali tarbiyya tana rayuwa ne a cikin kusanci, tattaunawa da zama tare.
A Part 3, za mu tattauna hanyoyi masu amfani da iyaye za su bi domin Karɓo Tarbiyyar Yaran Su Daga Hannun TV Da Wayar Salula