Malamin Aji

Malamin Aji Domin bada shawarwari akan Lafiya da Zamantakewa. For adverts and promotions, kindly contact us on WhatsApp: 07048758353
(1)

06/09/2026

SANARWA GA DUK MASU BIBIYAR WANNAN SHAFI

Karanta a nutse.

Ina sanar da ku cewa zan ci gaba da wallafa muhimman bayanai da s**a shafi lafiya, ilimi da sauran batutuwan da nake ganin ya dace mu fahimta a rayuwarmu.

Amma ina so in yi wani sabon bayani game da amsa tambayoyin mutum ɗaya bayan ɗaya.

A wasu lokuta, tambaya guda tana iya ɗaukar min lokaci mai tsawo. Ba wai kawai karanta tambayar da rubuta amsa nake yi ba. Wani lokaci ina duba tarihin matsalar, symptoms, results ko magungunan da aka ambata kafin in tsara amsa mai kyau.

Wasu lokutan ma ina ajiye wasu muhimman lokuta nawa domin in tsaya in saurari saƙonnin mutane da kuma ba su amsa. Wannan yana ɗaukar min lokaci sosai, kuma wani lokacin har ina rasa wasu muhimman lokuta a rayuwata.

Saboda haka, daga yanzu zan canza tsarin.

₦500 — BASIC CONSULTATION

Ga matsala ko tambaya mai sauƙi wanda ba ya buƙatar dogon assessment.

₦1,000 — FULL CONSULTATION

Ga matsalolin da suke buƙatar cikakken tarihin mutum, nazarin symptoms, results, magungunan da aka yi amfani da su da kuma ƙarin medical guidance.

Idan bayan duba bayanan matsalar na ga cewa case ɗin ya fi ƙarfin Basic Consultation, za a sanar da mutum kafin a ci gaba da consultation ɗin, domin ya koma Full Consultation na ₦1,000.

Amma zan ci gaba da yin rubuce-rubucen lafiya da sauran abubuwan muhimmanci kyauta domin wayar da kan al’umma.

Na tsara wannan tsarin ne domin in rage yawan saƙonnin da ba su da muhimmanci, sannan in samu damar ba waɗanda suke serious isasshen lokaci da cikakkiyar kulawar da ta dace.

Kuma consultation na mutum ɗaya zai shafi matsala ɗaya. Idan akwai wata matsala daban, za a yi mata sabon consultation.

Kafin a fara consultation, za a sanar da mutum irin consultation ɗin da matsalarsa ta dace da shi.

Kuma k**ar yadda na saba, ba zan taɓa wallafa tambayar mutum da amsar da na ba shi a shafina ba sai da izininsa da amincewarsa.

Na gode sosai da fahimta, goyon baya da amincewar da kuke yi da ni.

Malamin Aji ✍️
Whatsapp: 07048758353

Abin da zai iya faruwa shi ne ma’auratan sun shafe shekaru 10 ba tare da samun ciki ba saboda matsalar haihuwa daga nami...
06/09/2026

Abin da zai iya faruwa shi ne ma’auratan sun shafe shekaru 10 ba tare da samun ciki ba saboda matsalar haihuwa daga namiji, daga mace, daga bangarorin biyu, ko kuma ba a gano tak**aiman dalili ba. A wasu lokuta kuma akwai abin da ake kira subfertility—wato damar samun ciki tana nan, amma tana sa wahala ko tana ɗaukar lokaci.

Misali:

Mace na iya samun matsalar fitar ƙwai ko toshewar tubes.

Namiji na iya samun ƙarancin s***m ko matsalar motsin s***m.

A wasu ma’auratan, duk gwaje-gwajen suna iya zama ba su nuna wata matsala ba, amma ciki ya yi wahala.

Lokacin saduwa da lokacin ovulation da yawan saduwa ma suna da muhimmanci.

Saboda haka, idan bayan rabuwar aure mutumin ya sake aure ya samu ɗa, matar ma ta sake aure ta samu ɗa, hakan ba ya tabbatar da cewa ɗayan ne yake da matsalar haihuwa tun farko.

Wataƙila matsalar ta kasance daga ɗaya daga cikinsu, ko daga dukkansu, ko kuma wani yanayi ne na musamman da ya shafi wannan haɗin ma’auratan. Misali, idan s***m ɗin namiji yana da rauni sosai, samun ciki na iya zama da wuya da wata mace, amma ba zai zama ba zai yiwu ba; haka ma mace mai ƙarancin fertility na iya samun ciki daga baya.

Abin da wannan labarin ya fi koya mana shi ne: rashin samun ciki na tsawon shekaru ba ya k**ata a ɗora laifi kai tsaye kan mace ko namiji ba tare da an binciki su duka ba. A likitanci, ana binciken ma’auratan gaba ɗaya.

Kuma samun ciki cikin shekara ɗaya bayan sake aure ba yana nufin an gano ainihin dalilin rashin haihuwar shekarun baya ba. Sai dai idan an yi gwaje-gwaje a lokacin kuma an gano tak**aiman matsala.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

🤫 Sirrin da mutane da yawa basu sani ba...

Zaka iya samun 1GB daga ₦300 kacal a StrongMB.

🎁 Register yau ka samu ₦200
🎁 Saka MALAMINAJI a Invitation Code

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

Strongmb araha da inganci

Wannan maybe, ba a dade da yaye shi ba
05/09/2026

Wannan maybe, ba a dade da yaye shi ba

04/09/2026

Ba gaskiya ba ne cewa duk masu jini O+ suna yawan kamuwa da malaria.

Akwai wasu bincike da s**a nuna cewa blood group O na iya samun wani ɗan kariya daga kamuwa da severe malaria idan aka kwatanta da wasu blood groups, amma hakan ba yana nufin masu O+ ba sa kamuwa da malaria, kuma ba yana nufin za su riƙa kamuwa da ita akai-akai ba.

Idan kana yawan samun abin da kake ganin malaria ce, bai k**ata a danganta shi da O+ kawai ba. Yana da kyau a tabbatar da malaria da RDT ko blood film kafin shan maganin malaria, domin zazzabi da ciwon kai, kasala ko sanyi na iya kasancewa daga wasu infections daban.

Idan kana yawan samun malaria da aka tabbatar da gwaji akai-akai, to ya dace a binciki dalilin da ya sa hakan ke faruwa da kuma irin wurin da kake zama/ayyukan da kake yi, tare da ƙara matakan kariya daga sauro.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Wasu suna siyan 1GB a ₦600+,
amma masu amfani da StrongMB suna samu daga ₦300 kacal.

Me yasa zaka biya fiye da kima?

🎁 ₦200 Welcome Bonus
🎁 Invitation Code: MALAMINAJI

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

Babu k**ar Datar strongmb

“APOLO” da ake kira a nan yawanci conjunctivitis ne, wato kumburin fatar da ke rufe farin ido. Sau da yawa yana kasancew...
03/09/2026

“APOLO” da ake kira a nan yawanci conjunctivitis ne, wato kumburin fatar da ke rufe farin ido. Sau da yawa yana kasancewa viral, kuma yana da saurin yaɗuwa daga mutum zuwa mutum. Shi ya sa ake ganin mutane da yawa suna kamuwa a lokaci guda.

Domin kare kai:

Ka riƙa wanke hannu da sabulu sosai, musamman kafin ka taɓa ido.

Kada ka taɓa ko ka goge idonka da hannun da bai wanku ba.

Kada ka raba tawul, handkerchief, pillowcase ko kayan shafa ido da wanda yake da matsalar.

Kada ka yi amfani da eye drops ɗin wani mutum.

Idan ka kamu, ka guji taɓa idonka sannan ka taɓa wasu mutane ko kayan da ake amfani da su tare.

Ka daina amfani da contact lenses har sai ido ya warke gaba ɗaya.

Idan ka kamu, ba kowane Apollo ne yake buƙatar antibiotic ba. Idan viral ne, yawanci yana warkewa da kansa cikin kwanaki zuwa makonni. Za a iya amfani da artificial tears/lubricating eye drops da cold compress domin rage ƙuna, kaikayi da rashin jin daɗi.

Kada ka yi amfani da steroid eye drops da kanka. Haka kuma kada ka fara antibiotic eye drops sai likita ya duba ido ya ga akwai dalilin amfani da su.

Amma idan akwai matsanancin ciwon ido, tsananin jin haske, gani ya fara dusashewa, kumburi mai tsanani, ko wani abu ya shiga ido, a je wajen likitan ido da wuri domin waɗannan ba alamomin da ya k**ata a ɗauka cewa Apollo kawai ba ne.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

❓ Har yanzu kana siyan 1GB a sama da ₦600?

A StrongMB, zaka samu 1GB daga ₦300 kacal.

🎁 ₦200 Welcome Bonus
🎁 Saka MALAMINAJI a Invitation Code

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

Strongmb Data mafi inganci

Ba za a iya gane daga k**annin nonon mace ko girmansa cewa za ta iya shayar da jariri sosai ko a’a ba. Babban nono ko ƙa...
02/09/2026

Ba za a iya gane daga k**annin nonon mace ko girmansa cewa za ta iya shayar da jariri sosai ko a’a ba. Babban nono ko ƙaramin nono ba shi ne ke tabbatar da yawan madara ba.

Rashin wadatar nono na iya faruwa saboda dalilai daban-daban, k**ar:

Jariri bai k**a nono yadda ya k**ata ba

Ba a yawan sa jariri ya sha nono ba, musamman a farkon kwanaki da makonni

Jariri ba ya tsotsar nono sosai

Ana fara ba jariri formula da yawa, sai jariri ya rage tsotsar nono, wanda zai iya rage samar da madara

Wasu matsalolin hormone ko thyroid

Wasu magunguna ko wasu yanayin rashin lafiya

A wasu mata, wanda ba kasafai ba, akwai ƙarancin ƙwayoyin da ke samar da madara a nono

Saboda haka, idan a da yaran matarka ba sa samun isasshen nono, ya k**ata a binciki ainihin dalilin kafin a ce jikinta ba ya iya samar da madara. Likitan yara ko ƙwararren mai taimakawa wajen shayarwa zai iya duba yadda jariri yake k**a nono, nauyin jariri da kuma ko madarar tana wadatar sa.

Shawara: idan tana da wani sabon jariri a yanzu ko tana shirin haihuwa, a nemi taimakon likita ko lactation specialist tun daga farkon kwanaki bayan haihuwa. Akwai lokuta da za a iya gyara matsalar sosai.

Kuma game da ƙara aure saboda wannan dalili: babu wata hanyar da za ka tabbatar tun kafin aure cewa mace za ta samar da wadatacciyar madara ko ba za ta samu matsalar shayarwa ba. Wannan ba abu ne da ake iya hango shi daga siffar nono ko girman nono ba.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

📢 Data mai araha ta iso!

1GB daga ₦300 kacal a StrongMB.

✅ Mai sauri
✅ Mai inganci
✅ Farashi mai rahusa

🎁 ₦200 Welcome Bonus
🎁 Invitation Code: MALAMINAJI

Website 🌐 https://strongmb.ng/malaminaji

App 📲 https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB Data me nagarta

A bangaren likitanci:Ruwan da mace ke fitarwa yayin jima’i ba lallai ya kasance abu guda ba. Akwai:Lubrication: ruwan da...
01/09/2026

A bangaren likitanci:

Ruwan da mace ke fitarwa yayin jima’i ba lallai ya kasance abu guda ba. Akwai:

Lubrication: ruwan da ke ƙara yawa yayin tashin sha’awa domin rage gogayya. Wannan normal ne.

Female ej*******on: ƙaramin adadin ruwa da wasu glands da ke kusa da urethra ke fitarwa.

Squirting: ruwa mai yawa da kan fito ta urethra yayin jima’i; bincike ya nuna cewa yana iya samun babban bangare daga mafitsara, tare da wasu sinadarai daga glands na kusa da urethra.

Saboda haka, ba s***m na namiji ba ne, kuma ba a ce ruwa ɗaya ne a duk mata ba.

A bangaren Musulunci:

A nan ya k**ata a bambanta tsakanin mani, madhy da sauran ruwan jiki.

1. Maniyyi (mani): idan mace ta samu inzali sannan maniyyi ya fito, idan aka tabbatar shi ne mani, akwai hukuncin ghusl.

2. Madhy: ruwa ne mai ɗan siriri da kan fito saboda tashin sha’awa kafin inzali. Wannan ba ya wajabta ghusl, amma ana wanke wajen da ya taɓa sannan a yi alwala.

3. Lubrication/ruwan farji na yau da kullum: ba za a kira duk wani ruwa da mace ta gani yayin jima’i “mani” ba. Hukuncinsa yana da ƙarin bayani gwargwadon irin ruwan da yadda ya fito.

Saboda haka, ba duk ruwan da mace ke fitarwa yayin jima’i ne najasa ba, kuma ba dukkaninsu ne suke wajabta ghusl ba.

Idan ana magana ne musamman kan squirting mai yawa, akwai ɗan bambanci tsakanin malaman fikihu game da yadda za a tantance shi.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Shin ko kasan cewa 1GB ba sai ka siya a ₦600+ ba?

A StrongMB, zaka iya samun 1GB daga ₦300 kacal.

🎁 Register yau ka samu ₦200 Bonus
🎁 Ka saka MALAMINAJI a Invitation Code

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB — Babu k**ar mu.

Idan ma’aurata sun yi shekara 3 da aure kuma suna yin jima’i ba tare da amfani da hanyar hana ɗaukar ciki ba amma ba a s...
31/08/2026

Idan ma’aurata sun yi shekara 3 da aure kuma suna yin jima’i ba tare da amfani da hanyar hana ɗaukar ciki ba amma ba a samu ciki ba, ana iya ɗaukar hakan a matsayin matsalar rashin haihuwa (infertility), kuma bai k**ata a ci gaba da jira kawai ba. Ya k**ata su fara cikakken bincike a wurin likitan mata ko fertility specialist.

Muhimmin abu shi ne a binciki miji da mata tare, domin matsalar na iya kasancewa daga ɓangaren namiji, mace, ko kuma duka biyun.

A wajen miji, daga cikin gwaje-gwajen farko akwai:

Semen Analysis domin duba yawan s***m, motsinsu da sauran ingancinsu.
Likita na iya ƙara gwajin hormones ko scrotal ultrasound idan SFA ya nuna matsala.
A wajen mata, ana iya duba:

Shin tana yin ovulation, wato fitar ƙwai?
Pelvic ultrasound domin duba mahaifa da ovaries.
Hormonal tests k**ar TSH da prolactin, sannan sauran hormones gwargwadon ranar al’ada.
A duba ko fallopian tubes suna buɗe, musamman ta hanyar HSG, idan likita ya ga ya dace.
Wasu lokuta ana binciken mahaifa da sauran abubuwan da za su iya hana ciki.
Ba zai dace su ɗauka cewa matsalar daga mace ce kawai ko namiji kawai ba. Kuma bai k**ata su dogara da maganin gargajiya ko supplements kawai ba tare da sanin ainihin dalili ba.

A shekara 3 ba tare da samun ciki ba, shawarar da ta fi dacewa ita ce ku je tare wajen Gynecologist/Fertility specialist su fara tsarin bincike. Da zarar an gano dalili, sai a san ko ana bukatar magani, gyaran matsalar hormones, tiyata idan akwai wani abu k**ar varicocele ko matsalar tubes, ko kuma wasu hanyoyin taimakon haihuwa.

Kuma ku tuna: shekara 3 da rashin ciki ba yana nufin ba za ku taɓa samun haihuwa ba. Akwai dalilai da yawa masu magani, amma mataki na farko shi ne a gano ainihin dalilin.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

Har yanzu kana kashe kuɗi sosai wajen siyan data?

A StrongMB, zaka samu 1GB daga ₦300 kacal.

🎁 ₦200 Welcome Bonus
🎁 Saka MALAMINAJI a Invitation Code

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB — Data mai araha, babu ɓata lokaci.

Tambayar farko: ƙanƙantar kan nono (ni**le) ba lallai yana nufin akwai matsala ba. Girman nono da girman ni**le abubuwa ...
30/08/2026

Tambayar farko: ƙanƙantar kan nono (ni**le) ba lallai yana nufin akwai matsala ba. Girman nono da girman ni**le abubuwa biyu ne daban. Mace na iya kasancewa da manyan nonuwa amma ni**les ɗinta ƙanana. Haka kuma ni**le na iya canzawa ko ɗan fito wa a lokuta daban-daban saboda sanyi, taɓawa, motsawar jiki ko canjin hormones.

Lokacin pregnancy da bayan haihuwa kuma, hormones na iya sa nonuwa da ni**les su canza girma ko launi, sannan su ƙara fitowa. Amma ba lallai sai sun canza sosai ba. Idan nonon yana lafiya kuma babu ƙulli, ciwo mai ɗorewa ko wani ruwa/jini da yake fita ba tare da dalili ba, ƙanƙantar ni**le kaɗai ba matsala ba ce.

Game da tambayarka ta biyu, mace ba lallai sai ta yi ej*******on ko kuma ta fitar da wani ruwa domin a ce ta ji daɗin saduwa ko ta kai or**sm. Haka kuma jikewar farji na iya bambanta daga lokaci zuwa lokaci, kuma ba duk mace ce take jika sosai a kowane lokaci ba.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne idan tana jin daɗi ko kuma tana jin bushewa da zafi yayin saduwa. Idan tana jin bushewa ko ciwo, yana da kyau a ƙara lokacin wasanni da motsa sha’awa kafin saduwa, sannan idan ya zama dole za a iya amfani da water-based lubricant.

Game da ɗaukar ciki kuwa, rashin jikewa ko rashin ej*******on nata ba bazai hana ciki ba. Domin ciki yana samuwa ne idan maniyyin namiji mai ɗauke da s***m ya shiga farji sannan s***m ya kai ga ƙwai a lokacin da mace ke ovulation.

Saboda haka mace za ta iya ɗaukar ciki ko da ba ta ji or**sm ba, ba ta yi ej*******on ba, ko kuma ba ta ji jikewa sosai ba.

Amma tunda kana cewa tana jin k**ar tana kaiwa or**sm ne bayan kun gama kuma kana fita daga jikinta, hakan ma yana iya faruwa. Wasu mata suna buƙatar motsawa ta wasu hanyoyi ko kuma suna kaiwa or**sm a hankali bayan an gama saduwa. Ba lallai hakan yana nuna matsala ba.

Malamin Aji ✍️
Gmail: [email protected]

🔥 1GB a ₦300 kacal!

Me yasa zaka siya a ₦600+ alhali zaka samu mafi arha a StrongMB?

🎁 ₦200 Welcome Bonus
🎁 Saka MALAMINAJI a Invitation Code domin ƙarin bonus

🌐 Website 👇
https://strongmb.ng/malaminaji

📲 App 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.strongmb.app&referrer=MALAMINAJI

StrongMB — Data mai araha, saurin aiki

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malamin Aji posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share